Buhari ya ware wa matasan Najeriya rana ta musamman

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ayyana ranar 1 ga watan Nuwamban kowace shekara a matsayin ranar matasa ta kasa wato National Youth Day. Shugaban Kasar ya ware rana ce musamman domin taya matasa murna da yin nazari a kan matsalolin da suka shafe su da kuma gano hanyoyin da za a bi wajen warware su. […]

Buhari ya ware wa matasan Najeriya rana ta musamman

Shugaba Buhari a fadar Shehun Borno

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ayyana ranar 1 ga watan Nuwamban kowace shekara a matsayin ranar matasa ta kasa wato National Youth Day.

Shugaban Kasar ya ware rana ce musamman domin taya matasa murna da yin nazari a kan matsalolin da suka shafe su da kuma gano hanyoyin da za a bi wajen warware su.

Ministan Wasanni da Cigaban Matasa, Sunday Dare, shi ne ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter jim kadan bayan kammala zaman Majalisar Zartarwa na Tarayya wanda aka gudanar a ranar Laraba, 2 ga watan Satumba.

Ga abinda Mista Dare ya wallafa: “Yayin taron majalisa, Shugaba Buhari ya ba da lamunin ware duk ranar 1 ga watan Nuwamba na kowace shekara domin taya matasa murna, da gano hanyoyin warware matsalolin da suke fuskanta.

“Shugaban kasar a koda yaushe yana sadaukar da kai don ganin gwamnatinsa ta jajirce wajen kawo tsare-tsaren da za su amfani matasa. Na gode”.