Buhari ya yaba wa ’yan Najeriya kan addu’o’in da suke yi wa gwamnatinsa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yaba wa al’ummar kasar nan kan goyon baya da hadin kan da suke bai wa gwamatinsa duk da matsanancin halin da ake ciki. Shugaban kasar ya yi wannan yabo ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron kaddamar da Gidauniyar Raya Ilimi da kungiyar Jama’atu Izalatill Bidi’ah Wa Ikamatis […]

Buhari ya yaba wa ’yan Najeriya kan addu’o’in da suke yi wa gwamnatinsa
Buhari ya yaba wa ’yan Najeriya kan addu’o’in da suke yi wa gwamnatinsa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yaba wa al’ummar kasar nan kan goyon baya da hadin kan da suke bai wa gwamatinsa duk da matsanancin halin da ake ciki.
Shugaban kasar ya yi wannan yabo ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron kaddamar da Gidauniyar Raya Ilimi da kungiyar Jama’atu Izalatill Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa (JIBWIS) ta gudanar a Abuja a ranar Lahadin da ta gabata.
Shugaban Buhari wanda Ministan Birnin Tarayya, Abuja, Alhaji Muhammad Musa Bello, ya wakilta ya nuna farin cikinsa kan addu’o’in neman zaman lafiya da inganta tsaro da tattalin arzikin kasa da ’yan Najeriya suke yi a fadin kasar nan.
Ya yi kira ga ’yan Najeriya su ci gaba da ba da irin wannan gudunmawa har Allah Ya sa wannan gwamnati ta cimma manufofin da ta sanya a gaba na farfado da tattalin arzikin kasa.
Daga nan yaba wa kungiyar kan kokarin da take yi na gina babbar cibiyar addinin Musulunci a Abuja.
A jawabin tsohon Gwamnan Jihar Neja Alhaji Babangida Aliyu ya yi kira ne ga shugabannin addinin Musulunci na kasar nan kan su hada kansu su manta da bambance-bambancen kungiyanci don inganta karantarwar addinin Musulunci a kasar nan. Ya ce Musulmi za su samu damar yi wa addinin Musulunci aiki ne kawai idan suka hada kansu.
A jawabin Shugaban Taron Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar, ya yaba wa Shugaban kungiyar Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir, kan kokarin da kungiyar ke yi na ilimantar da al’ummar kasar nan. Ya ce wannan gagarumin aiki da kungiyar take yi yana karfafa wa matasa gwiwa wajen neman ilimin addini da na zamani.
Sarkin Musulmin wanda Sarkin Abaji kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Birnin Tarayya Abuja, Alhaji Adamu Yunusa ya wakilta, ya bukaci Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi su rika taimakawa wajen ilimantar da matasa, don samun al’umma tagari.
Tun da farko a jawabin Sheikh Sani Yahya Jingir, ya ce daga lokacin da aka kafa kungiyar zuwa yanzu shekara 38 da suka gabata, ta samu nasarar gina dubban makarantu da masallatai a ciki da wajen Najeriya.