Buhari ya yi alhinin mutuwar Fasto TB Joshua
Joshua ya rasu bayan wani wa’azi da ya halarta a Muja,i’arsa ta Synagogue da ke Legas.
Shugaba Muhammadu Buhari ya jajanta wa iyalai da mabiya Mujami’ar Synagogue dangane da rasuwar Fasto Temitope Balogun wanda aka fi sani da TB Joshua.
Buhari ya aike da sakon ta’aziyyarsa cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Mista Femi Adesina ya fitar ranar Lahadi a Abuja, babban birnin Najeriya.
- Jirgin kasa ya kashe mutum daya a Makkah
- Zan kawo karshen rikicin Fulani da Makiyaya a Najeriya — Yariman Bakura
Sakon shugaban kasar ya ce za a yi kewar bajimin malamin na Kirista musamman mabiyansa da kuma duniya baki daya kan gudunmuwar da ya bai wa mutane ta hanyar ayyukansa na taimako a yayin da yake raye.
Shugaban kasar ya nemi mabiyan mamacin da su dauki dangana ta hanyar riko da ilimin da suka samu a wurinsa da bai zai taba misaltuwa ba.
Ya kuma jajanta wa gwamnati da mutanen Jihar Ondo kan wannan rashi da suka yi tare da rokon Ya Mai Duka ya jikansa.
A yau Lahadi ce Mujami’ar Synagogue da ke birnin Legas ta sanar da rasuwar Fasto Joshua wanda shi babban limaminta kuma wanda ya assasata.
Mujami’ar ta ce Joshua ya rasu ne bayan wani wa’azi da ya halarta a cikinta wanda aka yi da yammacin Asabar kamar yadda aka saba.
Rahotanni sun ce TB Joshua ya rasu yana da shekaru 57 a duniya.