Buhari ya yi alhinin mutuwar Shugaban Jami’ar NOUN na farko
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi alhinin mutuwar Shugaban Jami’ar Karatu Daga Gida ta Najeriya (NOUN) na farko, Farfesa Gabriel Jimoh Afolabi Ojo. Shugaban Kasar cikin wani sako mai dauke da sa hannun hadiminsa kan harkokin sadarwa, Femi Adesina, ya taya ’yan uwa da abokanan arziki jimamin mutuwar Farfesa Ojo. Farfesa Ojo ya riga mu […]
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi alhinin mutuwar Shugaban Jami’ar Karatu Daga Gida ta Najeriya (NOUN) na farko, Farfesa Gabriel Jimoh Afolabi Ojo.
Shugaban Kasar cikin wani sako mai dauke da sa hannun hadiminsa kan harkokin sadarwa, Femi Adesina, ya taya ’yan uwa da abokanan arziki jimamin mutuwar Farfesa Ojo.
Farfesa Ojo ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 90 a duniya wanda ajali ya katse masa hanzari a ranar Lahadi, 30 ga watan Agusta.
- Karin kudin lantarki: Atiku ya kwance wa Buhari zani a kasuwa
- Tsohon Ministan Najeriya daga jihar Kano ya riga mu gidan gaskiya
Mai yankan kauna ta tari hanzarin Farfesa Ojo yana tsaka da bacci a gidansa da ke Ikeja a birnin Iko.
Tarihi ya tabbatar da cewa, Marigayi Ojo da ya shafe rayuwarsa wajen yi wa ilimi hidima musamman fannin nazarin kasa wato Geography ta hanyar koyo da karantarwa, ya wallafa littafai da mujallun ilimi fiye 140.
Ya kasance shugaban kwamitin riko da gudanarwa a tsarin karatu daga gida na Najeriya daga shekarar 1980 zuwa 1981.
Marigayi Ojo shi ne Shugaban Jami’ar NOUN na farko wanda aka nada daga shekarar 1981 zuwa 1984.