Buhari ya yi alhinin mutuwar gwamnan tsohuwar jihar Arewa Maso Yamma
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jajanta wa ’yan uwa, makusanta da abokan huldar tsohon gwamnan farko na jihar Arewa maso Yamma a mulkin soja, Alhaji Usman Faruk wanda ajali ya katse masa hanzari a ranar Juma’a. Shugaban Kasar cikin wani sako da ya fitar ta bakin mai magana da yawunsa, Mallam Garba Shehu, ya kuma […]
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jajanta wa ’yan uwa, makusanta da abokan huldar tsohon gwamnan farko na jihar Arewa maso Yamma a mulkin soja, Alhaji Usman Faruk wanda ajali ya katse masa hanzari a ranar Juma’a.
Shugaban Kasar cikin wani sako da ya fitar ta bakin mai magana da yawunsa, Mallam Garba Shehu, ya kuma mika ta’aziyyarsa zuwa ga Gwamnati da al’ummar jihar Gombe dangane da wannan rashi.
- Yadda na rayu a kurukuku kwana 5 —Sanata Ndume
- An nada tsohon Kwamishinan Kudi Surajo Garba a matsayin Galadiman Karaye
Shugaba Buhari ya ce tsohon Kwamishinan ’Yan Sandan a yayin rayuwarsa ya ba da gudunmuwar tabbatar da hadin kan kasar nan.
Kazalika, Shugaba Buhari ya ce marigayi Alhaji Faruk ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimtawa al’ummarsa har bayan ya yi ritaya daga aiki, inda ya misalta mamacin a matsayin mutum mai kankan da kai kuma mai kirki na hakika.
Ya yi addu’ar Allah ya jikansa da Rahama kuma Ya yi masa sakayya da kyakkyawar makoma.
Mai magana da yawun shugaban kasar ya ce an gudanar jana’izar tsohon kwararren jami’in tsaron a yau Juma’a.
Marigayi Alhaji Usman Faruk wanda aka haifa a shekarar 1935, shi ne tsohon jihar Arewa ta Yamma na farko daga shekarar 1967 zuwa 1975 a zamanin mulkin soja karkashin jagorancin tsohon Shugaban Janar Yakubu Gowon.