Buhari ya yi ganawar sirri da Gwamnoni kan karin albashi
Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta yi gana da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari akan batun karin karancin albashin ma’aikatan kasar wanda aka yi a fadar shugaban kasa a Abuja. Gwamnoni hudu da suka halarci ganawar sirri sun hada da: Gwamnan Legas Akinwunmi Ambode, Gwaman Enugu Ifeanyi Ugwuanyi da Gwamnan Kebbi Atiku Bagudu da Gwamnan jihar Zamfara […]
Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta yi gana da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari akan batun karin karancin albashin ma’aikatan kasar wanda aka yi a fadar shugaban kasa a Abuja.
Gwamnoni hudu da suka halarci ganawar sirri sun hada da: Gwamnan Legas Akinwunmi Ambode, Gwaman Enugu Ifeanyi Ugwuanyi da Gwamnan Kebbi Atiku Bagudu da Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari .
A makon da ya gaba ta ne Gwamnatin Tarayya ta amince da Naira dubu 30 a matsayin mafi karancin albashi. Bayan wani tattaunawa da qungiyar Gwamnonin ta yi da kungiyar kwadago, wanda hakan yasa Gwamnonin suka mayar wa kungiyar martani akan cewa, ko dai a amince da albashin naira dubu 30 ko kuma a ajiye aiki.
Sai dai Gwamnonin basu bayyana wa manema labarai abin da aka tattauna ba na tsawon sa’a daya.