Buhari ya yi juyayin rasuwar dattijuwar da ta ba shi Naira miliyan daya
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yaba kyawawan halayen Hajiya Fati Koko da aka fi sani da Maitalle Tara, wadda ta rasu tana da shekara 95.Shugaba Buhari wanda ya mika sakon ta’aziyyar rasuwar dattijuwar wada ta yi zaman jiransa na awa tara a Birnin Kebbi a farkon bara lokacin da ya je yakin neman zabe domin […]
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yaba kyawawan halayen Hajiya Fati Koko da aka fi sani da Maitalle Tara, wadda ta rasu tana da shekara 95.
Shugaba Buhari wanda ya mika sakon ta’aziyyar rasuwar dattijuwar wada ta yi zaman jiransa na awa tara a Birnin Kebbi a farkon bara lokacin da ya je yakin neman zabe domin ta mika masa gudunmawar Naira miliyan daya, Buhari ya bayyana ta da “Mace mai kyakkyawan hali wadda ta tsaya kanabin da ta yi imani da shi, kuma ta sadaukar da rayuwarta a kai.”
Hajiya Fati Koko ta ba Buhari daukacin kudin da ta tara don tallafa wa kamfe dinsa a lokacin da yake takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APC, inda a lokacin ta ce gamsuwa da halin gaskiya da da’a da tsayuwa kan gaskiya ne suka sa take goyon bayan Buhari.
Lokacin da ya samu labarin rasuwarta Shugaba Buhari ya yaba wa Hajiya Fati Koko kan tsayuwar daka da sadaukarwarta, inda ya bukaci ’yan Najeriya su yi koyi da kyakkyawar rayuwarta.
“Ta bayar da kusan duk abin da ta mallaka domin yakin neman zabenmu. Duk da cewa shekarunta sun yi nisa, tana da imanin za a iya samun sabuwar Najeriya kuma ta bi fatarta da aiki. Dubi karfin halinta da karfin imaninta ga makomar kasarta. ’Yan Najeriya tsofaffi da matasa suna da abin koyi daga gare ta,” inji Shugaban kasar.
Shugaba Buhari ya mika ta’aziyya ga iyalai da dangin marigayiyar, inda ya bukaci su yi hakuri da wannan rashin wannan dattijuwa wadda ta yi tsawon kwana “kuma ta fara ganin canjin da ta dade tana nema.”
Shugaba Buhari ya mika ta’aziyya ga Gwamna da al’ummar Jihar Kebbi wadanda ya ce za su yi rashin kyawawan halayen Hajiya Fati Koko, ya ce, ya kamata “Rayuwarta ta kasance abar koyi wajen yi wa Allah hidima da kuma al’umma da kasa.” Kuma ya yi fatar Allah Ya sanya Aljanna ta zama makomarta.