Buhari ya yi ta’aziyyar rasuwar dan Abacha
Abdullahi ya rasu da sanyin safiyar ranar Asabar.
Shugaba Muhammadu Buhari ya yi ta’aziyyar rasuwar dan tsohon Shugaban Kasa a lokacin mulkin soji, Janar Sani Abacha.
Abdullahi wanda da ne na biyun karshe ga Abacha, ya rasu da sanyin safiyar Asabar yayin da yake barci.
Buhari ya aike da sakon ta’aziyyar ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu ya fitar, inda ya jajanta wa iyalan Abacha kan rasuwar Abdullahi.
Buhari ya yi addu’ar Allah Ya masa rahama ya kuma yafe masa kurakuransa.
Gumsu Sani Abacha, wadda mata ce ga Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, ita ce ta soma sanar da rasuwar dan uwan nata a shafinta na Twitter.
A cewar sakon Gumsu, “InnalilLahi wa inna ilaiHi raji’un. Na yi rashin dan uwana Abdullahi Sani Abacha.
“Ya rasu lokacin da yake barci. Allah Ya yi masa rahama ya yafe masa. Allah Ya sa Aljanna Firdaus ta zama makoma a gare shi.”
Abacha ya mulki Najeriya a lokacin mulkin soji, bayan da ya yi juyin mulki a 1993 har zuwa 1998.
Juyin mulkin da Abacha ya yi shi ne na karshe a tarihin Najeriya da aka yi a lokacin mulkin soji.