Buhari ya yi ta’aziyyar rasuwar Sarkin Gaya
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana jimaminsa game da rayuwa Sarkin Gaya, Alhaji Ibrahim Abdulkadir. A sakon Buhari na ta’aziyyar rasuwar Sarkin Gaya, mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya fitar, ya bayyana mamacin da cewa “yana daga cikin sarakunan kasar nan da suka kare mutucin sarautun gargajiya.” An yi jana’izar Sarkin Gaya, Alhaji Ibrahim […]
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana jimaminsa game da rayuwa Sarkin Gaya, Alhaji Ibrahim Abdulkadir.
A sakon Buhari na ta’aziyyar rasuwar Sarkin Gaya, mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya fitar, ya bayyana mamacin da cewa “yana daga cikin sarakunan kasar nan da suka kare mutucin sarautun gargajiya.”
- An yi jana’izar Sarkin Gaya, Alhaji Ibrahim Abdulkadir
- ’Yan bindiga daga Zamfara da Katsina sun fara kai hari Kano
Mutumin kirki ne da ya hidimta wa al’ummarsa da sadaukar da kai kuma za a jima ana tunawa da shi da hakan.
Ya kuma jajanta wa Masarautar Gaya al’ummar masarautar da kuma Gwamnatin Jihar Kano game da rasuwar tare da addu’ar Allah Ya gafarta masa Ya kuma rahamshe shi.