Buhari ya yi taro da shugabannin APC don ya kawar da fargaba
Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da shugabannin jam’iyyar APC don ya kawar da fargabar ’yan jam’iyyar a yayin da shugabannin jam’iyyar ke yin taron a yau. Wata majiya da ke cikin taron ta fada wa Aminiya cewa shugaban kasa ne ya jagoranci taron don ya kawar da fargabar da ake da ita na tayar da […]

Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da shugabannin jam’iyyar APC don ya kawar da fargabar ’yan jam’iyyar a yayin da shugabannin jam’iyyar ke yin taron a yau.
Wata majiya da ke cikin taron ta fada wa Aminiya cewa shugaban kasa ne ya jagoranci taron don ya kawar da fargabar da ake da ita na tayar da jijiyar wuya.
A ranar Lahadin da ta gabata wasu membobin kungiyar kamfe na shugaban kasa na jam’iyyar APC na shekarar 2015 wadanda suke yi wa Shugaba Buhari biyayya sun fada wa Aminiya cewa sun gano wata makarkashiyar da wasu ’yan jam’iyyar suka yi fushi suka shirya don yi wa Buhari kwantan-Bauna a taron da za a yi yau.