Buhari ya yi wa Kasar Kuwait ta’aziyya kan rasuwar Sarkinta
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi alhinin mutuwar sarkin Kuwait, Sheikh Sabah al-Ahmad Al-Jaber Al-Sabah. Sakon ta’aziyyar Shugaban Kasar na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Mallam Garba Shehu ya fitar a ranar Laraba. An rantsar da sabon Sarki a Kuwait Sarkin Kuwait Sheikh Sabah al-Ahmed ya mutu yana da shekaru […]
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi alhinin mutuwar sarkin Kuwait, Sheikh Sabah al-Ahmad Al-Jaber Al-Sabah.
Sakon ta’aziyyar Shugaban Kasar na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Mallam Garba Shehu ya fitar a ranar Laraba.
Shugaba Buhari ya janjanta wa Gwamnati da daukacin al’ummar kasar Kuwait dangane da rasuwar Sarkin wanda ajali ya katse masa a ranar Talata.
Buhari ya jinjina wa Marigayin Sarkin wanda a cewarsa ya jijirce wajen tabbatar da zaman lafiya da hadin kai tsakanin Kasashen da ke yankin Gulf a tsawon shekaru 14 a ya shafe a karagar mulki.
Kazalika shugaban kasar ya taya sabon sarkin Kuwait, Sheikh Nawaf Al-Ahmad Al-Jaber Al-Sabah, murna wanda aka nada kwana daya bayan mutuwar yayansa.
Buhari ya nemi Sheikh Nawaf da ya yi koyi da kyawawan tsare-tsare da akidu irin na dan uwansa wajen kara wa dangartakar da ke tsakanin Najeriya da Kuwait karfi.