Buhari ya yi watsi da bukatar ‘yan majalisa ta sauya dokar zabe
A ranar Talatar ce Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi watsi da matakin da Majalisar Dokoki ta kasa ta dauka, na sake fasalin jadawali zabubbukan 2019. Shugaba Buhari ya aike wa Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki da takwaransa na Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara da wasikar da ke kunshe da bayani kan dalilin yin watsi da […]

A ranar Talatar ce Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi watsi da matakin da Majalisar Dokoki ta kasa ta dauka, na sake fasalin jadawali zabubbukan 2019. Shugaba Buhari ya aike wa Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki da takwaransa na Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara da wasikar da ke kunshe da bayani kan dalilin yin watsi da bukatar sauya dokokin zaben.
Wasikar wacce aka karanta ta a dukan zaurukan majalisar biyu a yayin zamansu na ranar Laraba, Shugaban kasar ya bayyana dalilansa na kin amincewa da kwaskwarimar dokar zaben da majalisar ta yi, yana mai cewa sashe na 25 na dokokin zabe, ya bai wa Hukumar INEC cikakkiyar damar tsarawa tare da gudanar da zabubbuka a kasar nan kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
Shugaba Buhari dai ya yi fatali da bukatar sauya dokokin zaben ne wanda ya bukaci fara gudanar da zaben ’yan Majalisar Tarayya kafin na Shugaban kasa. kudirin wanda tuni ya samu amincewar zaurukan majalisa.
Kodayake, ’yan Majalisar Dokokin sun ce sun sauya fasalin tsarin zaben 2019 ne domin bai wa Shugaban kasa damar sanya ido a zabubbukan. To amma wadansu masu sharhi a kan lamuran yau da kullum na ganin matakin da majalisar ta dauka, tamkar wata dama ce su ’yan majalisar na su samu damar lashe zabubbukansu sannan su yi watsi da Shugaban kasa.