Buhari ya zabi Okoye da wasu 25 don aikin hukumar INEC da ta kidaya
Shugaba Muhammadu Buhari jiya ya rubuta wa majalisar dattijai neman ta amince da nadin Lauya Festus Okoye a matsayin kwamishinan zabe a Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta INEC mai wakiltar Kudu Maso Gabas. Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ya karanta wasikar Buharin kan neman ta tabbatar da zaben Okoye a zaman majalisar na […]
Shugaba Muhammadu Buhari jiya ya rubuta wa majalisar dattijai neman ta amince da nadin Lauya Festus Okoye a matsayin kwamishinan zabe a Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta INEC mai wakiltar Kudu Maso Gabas.
Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ya karanta wasikar Buharin kan neman ta tabbatar da zaben Okoye a zaman majalisar na jiya.
Shugaban majalisar har ila yau ya karanta wasiku biyu na shugaban kasar da ke neman a tabbatar da zaben wasu mutanen.
A wasikar mai dauke da kwanan watan ranar 27 ga watan Maris, Buhari ya ce ya gabatar da sunan Okoye kamar yadda sashe na 154 karamin sashe na 1 da kundin dokokin Najeriya na shekarar 1999 ya tanada.
Okoye shi ne shugaban hukumar lura da hakkin dan adam wanda lauya ne a kotun koli ta Najeriya kuma mazaunin jihar Kaduna ne.
A wata wasikar, shugaban kasar ya bukaci majalisar ta amince da nadin Sanata Abba Ali daga mazabar Katsina ta Arewa maso yamma da Sanata Mohammed Sagir daga mazabar Arewa ta tsakiya ta jihar Neja a matsayin lauya na hukumar lura da bangaren shari’a ta tarayya.