Buhari ya ziyarci sojoji a Maiduguri
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bukaci sojojin Najeriya da sauran jami’an tsaro kada su yi kasa- a- gwiwa wajen yakin da suke yi don tabbatar da dorewar kasar tsintsiya-madaurinki-daya. Da yake yi wa sojojin da ke fagen fama a yakin da kasar take yi da kungiyar Boko Haram jawabi a Maiduguri jiya, shugaban kasar ya […]
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bukaci sojojin Najeriya da sauran jami’an tsaro kada su yi kasa- a- gwiwa wajen yakin da suke yi don tabbatar da dorewar kasar tsintsiya-madaurinki-daya.
Da yake yi wa sojojin da ke fagen fama a yakin da kasar take yi da kungiyar Boko Haram jawabi a Maiduguri jiya, shugaban kasar ya jaddada kudurin gwamnatin kasar na ci gaba da mara musu baya.
Ya ce “Hakika kuna yin daya daga cikin muhimman ayyukan bautawa kasa. Ya zama wajibi ku tsaya kyam ku bautawa kasarku. Tsaron kasar nan yana hannun Allah kuma yana hannun jami’an tsaron kasar nan. Idan ba ku tsaya ba ku ne za ku fi yin asara. Ina baku tabbacin cewa idan Najeriya ba ta ci gaba da dorewa ba jami’an tsaro ne za su fara shiga tsaka-mai-wuya. Saboda idan Najeriya ta wargaje ba wanda zai amince tsohon kanar ko janar na soja ya jagoranci kauyensu. Ba a ta zancen zai samu fansho ko garatuti”.