Buhari zai daidaita kome a kasar nan – Gwamna Oshiomhole
Gwamnan Jihar Edo Kwamared Adams Aliyu Oshiomhole ya bayyana wa taron ’yan jarida a hedikwatar karamar Hukumar Etsako ta Yamma, a wata ziyarar aiki da ya kai a yankin a karshen makon jiya cewa ya yi imanin cewa muddin Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana ci gaba da samun hadin kan ’yan Najeriya, to lallai zai […]
Gwamnan Jihar Edo Kwamared Adams Aliyu Oshiomhole ya bayyana wa taron ’yan jarida a hedikwatar karamar Hukumar Etsako ta Yamma, a wata ziyarar aiki da ya kai a yankin a karshen makon jiya cewa ya yi imanin cewa muddin Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana ci gaba da samun hadin kan ’yan Najeriya, to lallai zai samu nasara a kan burinsa da ya sa gaba, domin yana da kyakkyawar niyya na ganin ya daidaida kome a kasar nan ta yadda ’yan Najeriya za su samu kyakkyawar rayuwa.
Oshiomhole ya ce: “Na san Buhari yana da kyakkyawar manufa da aniya ta gyaran kasa, don haka zai yi aiki da zai kawo amfani a kasar nan kamar inganta hanyoyi, wutar lantarki da sauran muhimman ayyuka da za su taimaki rayuwar jama’ar kasa. Dalili shi ne, domin mun yi wani zama da shi Shugaban kasa a makon da ya gabata, inda ya nuna shi shugaba ne na talakwa. Ba ya nuna wani bambanci ko da kadan.”Ya ce shugaban ya ba su tabbacin cewa a gwamnatinsa za ta tabbatar da ya ba ’yan Najeriya tsaro da ababen more rayuwa. “Don haka na tabbatar da Buhari zai gyara mana kasar nan saboda wajibi ne mu yi hakuri, domin barnar da wasu suka yi a kasar nan ba karama ba ce, tana da girma sosai. Wannan ya sa ba za a iya gama komai a rana guda ba, saboda wancan tsohuwar gwamnatinmu ba ta bar komai a cikin asusun gwamnati ba amma da yardar Allah Najeriya za ta farfado har kowa sai ya yi mamaki. Don haka shawara ita ce, mu hada kanmu mu ba wannan gwamnati ta Buhari goyon baya da hadin kai na gaskiya.” Inji Gwamna Oshiomole.