Buhari zai gabatar da kasafin kudin 2022 ranar Alhamis
Majalisar ta bukaci Kwamitinta na Kudi ya gabatar mata da rahotonsa ranar Laraba.
Shugaba Buhari yayin da ya ke gabatar da kasafin 2020
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai gabatar wa Majalisar Dokoki ta Kasa da kudurin kasafin kudin 2022 a ranar Alhamis.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Ovie Omo-Agege, ne ya bayyana hakan a ranar Talatar a zauren majalisar.
- Majalisar Kano ta dakatar da gina shaguna a Masallacin Fagge
- A shirye Najeriya take ta taimaka wa Sudan ta Kudu — Buhari
“Za ku gabatar mana da rahotonku zuwa gobe (Laraba0, don ba mu damar nazartar gabatar da kasafin kudin a ranar Alhamis,” inji Omo-Agege.
Ya bukaci kwamitin harkokin kudi na majalisar da ya gaggauta aikin da yake yi kan tsare-tsaren kasafin, domin gabatar da rahotonsa a gaban majalisa zuwa ranar Laraba.
Bayan karanta takardar da Shugaban Kasar ya aike wa majalisar, shugabanta, Sanata Ahmad Lawan ya mika ta ga kwamitinin kasafin kudi.