Buhari zai kaddamar da gidaje 500 a Borno

A karo na uku Shugaba Buhari zai kai ziyarar aiki Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

Buhari zai kaddamar da gidaje 500 a Borno

Buhari yayin saukarsa a Abuja bayan dawowa daga Spain a ranar Juma’a, 3 ga watan Yunin 2022.

Shugaban Kasa Muhammad Buhari zai kai ziyara Maiduguri, babban birnin Jihar Borno domin kaddamar da wasu ayyuka da aka kammala a ranar Alhamis.

Karo na uku ke nan da shugaban kasar zai kai ziyara Jihar Borno, bayan zuwan da ya yi a watan Yuni da kuma watan Disamban 2021.

Ana sa ran a yayin ziyarar, Buhari zai kaddamar da gidajen malamai a unguwar Bulunkutu da kuma gidaje 500 da gwamnan jihar, Babagana Zulum ya gina wa ’yan gudun hijira a yankin Molai.

Zai kai ziyarar ban girma ga Fadar Shehun Borno, Umar Ibni Elkanemi.