Buhari zai kaddamar da kasafin kudi ranar Talata
Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da kasafin kudi na badi a gaban ‘yan Majalisar Dattawa da Wakilai. A wata wasika da Yakubu Dogara ya karanta a ranar Alhamis, Buhari ya bukaci ‘yan majalisun da su hadu a waje daya domin ya samu damar gabatar musu da kasafin kudin. Kuma wasikar ta nuna cewa shugaba […]
Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da kasafin kudi na badi a gaban ‘yan Majalisar Dattawa da Wakilai.
A wata wasika da Yakubu Dogara ya karanta a ranar Alhamis, Buhari ya bukaci ‘yan majalisun da su hadu a waje daya domin ya samu damar gabatar musu da kasafin kudin. Kuma wasikar ta nuna cewa shugaba Buhari zai kaddamar da kasafin kudin ne a ranar Talata 7 ga watan Nuwamba 2017 da misalin karfe biyu na rana.