Buhari zai kaddamar da tagwayen hanyoyi a Kurus Ribas

Gwamnar Jahair Kurus Riba Farfesa Ben Ayade na jam’iyar adawa ta PDP ya ce kwanan nan zai gayyaci shugaban kasa Muhammadu Buhari don ya kaddamar da tagwayan hanyoyi a jihar.Gwamnan ya furta haka a ganawar da ya yi da wakilan kafafen yada labarai dake aiki a jahar ranar laraba.“Nan ba da jimawa ba zan gayyato […]

Buhari zai kaddamar da tagwayen hanyoyi a Kurus Ribas
Buhari zai kaddamar da tagwayen hanyoyi a Kurus Ribas

Gwamnar Jahair Kurus Riba Farfesa Ben Ayade na jam’iyar adawa ta PDP ya ce kwanan nan zai gayyaci shugaban kasa Muhammadu Buhari don ya kaddamar da tagwayan hanyoyi a jihar.
Gwamnan ya furta haka a ganawar da ya yi da wakilan kafafen yada labarai dake aiki a jahar ranar laraba.
“Nan ba da jimawa ba zan gayyato shugaban kasa yazo kuros riba domin ya aza harsashin gina tagwayen hanyoyin mota da kuma wasu kanana da suka ratsa kuros riba zuwa makwabciyar jahar Binuwai domin saukaka zurga-zurgar ababen hawa da ta kasuwanci”. In ji gwamna Ayade.
Gwamnan  ya kara jaddada kudurin da  gwamnatinsa take da shi na baiwa shugaban kasa muhammadu Buhari goyon baya dari bisa dari domin gwamnatinsa ta samu nasara daci gaba.
“Zamu ci gaba da baiwa gwamnatin shugaban kasa muhammadu Buhari goyon baya domin ta samu nasara ba tare da  nuna masa banbancin jamiyya,  ko nuna masa adawa ba musamman irin yadda muka ga shugaban kasar ke kyautata mana ba tare da nuna ma kuros riba ba jahar da  jamiyyar  APC ke mulki b ace”.inji Ayade.
Haka kuma furofesa Ben. Ayade ,ya ci gaba da cewa “duk da matsalar karancin kaso daga gwamnatin tarayya da kuma na tattalin arzikin kasa da muke fama da shi amma hakan bai hana shugaban kasar mayar da hankalinsa kan bukatun jahar kuros riba ba.”