Buhari zai kafa kamfanonin casar shinkafa a Adamawa

Gwamnati za ta samar wa manoman da taraktoci kuma ta rika sayen shinkafa daga wurinsu.

Buhari zai kafa kamfanonin casar shinkafa a Adamawa

Gwamnatin Tarayya za ta kafa masana’antu uku na casar shinkafa a Jihar Adamawa a yunkurinta na bunkasa harkar noma da kudaden shigan masu kasuwancin noma a Najeriya.

Hukumar Inganta Kasasr Noma ta Najeriya (NALDA), ta ce hakan ya zama wajibi domin manoman Jihar Adamawa na noma shinkafa mai tarin yawa amma sai dai a kai ta wasu wurare domin casa.

Babban Sakataren Hukumar, Prince Paul Ikonne ya ce: “NALDA za ta kafa kamfanonin casar shinkafa domin kara daga darajar abin da manoman suke samarwa.

Ya ce, domin cimma hakan, NALDA za ta raba wa manoma ingantaccen irin shuka, taraktoci da malaman gona.

“Sannan hukumar za ta rika sayen amfanin da manoma suka girbe ta yadda za su samu riba domin kawo karshen ayyukan miyagun ’yan kasuwa,” inji shi.

Babban Sakaren ya ce Hukumar ta samu karin filin noma hekta 5,000 a garin Fulfulde a kan hekta 4,000 da take da shi a baya, da za ta yi amfani da shi.

Game da yadda manoma za su biya kudin taraktocin, ya ce: “Ba kudin za ku biya ba za, amma idan muka tashi sayen abin da kuka noma sai a rika cirar kudin amfanin da kuka yi da taraktocin.”

Prince Paul Ikonne ya ce kafa masana’antun na da naga cikin abin da taron tattaunawar gwamnati da manoman Jihar Adamawa ya cimma matsaya a kai.

Ya ce ya ziyarci Jihar Adamawa ne bayan umarnin Shugaba Buhari na cewa a je kowace jiha a inganta kasar nomanta ta yadda jama’a za su samu karin arzikin noma.