Buhari zai kara karbo bashin dala biliyan 5.5
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na neman amincewar Majalisar Dattawa domin karbo rancen dala biliyan 5.513. Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa za ta yi amfani da kudaden ne wurin aiwatar da ayyukan da ke cikin kasafin kudin 2020. Ya bayyana haka ne a wasikar da aka karanta a lokacin zaman Majalisar na yau Alhamis. Wasikar da […]
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na neman amincewar Majalisar Dattawa domin karbo rancen dala biliyan 5.513.
Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa za ta yi amfani da kudaden ne wurin aiwatar da ayyukan da ke cikin kasafin kudin 2020.
Ya bayyana haka ne a wasikar da aka karanta a lokacin zaman Majalisar na yau Alhamis.
Wasikar da Shugaban Majalisar Ahmad Lawan ya karanta ta ce za a samo rancen kudaden ne daga hukumomin kasahen duniya.
- A karon farko, an samu bullar coronavirus a Jihar Kogi
- Dalilin da ya sa ba a samu coronavirus a Kogi da Cross River ba
- Rage Albashi: ’Yan kwadago sun yi barazanar yajin aiki a Kano
Za a karbo kudaden ne daga Asusun Lamuni na Duniya (IMF), Bankin Duniya, Bankin Raya Afrika da kuma Bankin Musulunci.
Karin bayani na nan tafe…