Buhari zai karrama ’yan wasan Olamfik
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce zai karrama ’yan wasannin Olamfik da suka wakilci kasar nan a wasannin Olamfim na musamman da Amurka ta shirya wanda aka kammala kwanan nan a Los Angele da ke Amurka. Mai bai wa shugaban kasa shawara a kan harkokin jaridu da kuma wayar da kan al’umma Malam Garba Shehu […]
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce zai karrama ’yan wasannin Olamfik da suka wakilci kasar nan a wasannin Olamfim na musamman da Amurka ta shirya wanda aka kammala kwanan nan a Los Angele da ke Amurka.
Mai bai wa shugaban kasa shawara a kan harkokin jaridu da kuma wayar da kan al’umma Malam Garba Shehu ne ya sanar da haka a ranar Litinin da ta wuce a Abuja. Ya ce shugaban zai tarbe su don karrama su ne a fadar gwamnati da ke Abuja.
“Shugaban kasa ya bayyana farin cikinsa a kan namijin kokarin da ’yan wasan Olamfik din da suka wakilci kasar nan suka nuna bayan sun samu nasarar lashe lambobin yabo da dama a yayin gasar, ko shakka babu shugaban ya yi murna da su kuma zai karrama su”.
Su dai ’yan wasan na Olamfik din sun lashe lambobin yabo 71 ne a yayin gasar kuma 34 daga ciki lambobin zinare ne.
’Yan wasan sun haskaka a wasanni daban-daban da suka fafata a lokacin da gasar ke gudana al’amarin da ya sa suka lashe lambobin yabo har 71.
Wannan gasa dai ta musamman ce da Amurka ta shirya, inda ta gayyato kasashen duniya daban-daban ciki har da Najeriya don su fafata.
Ana sa ran tawagar Najeriyan za ta dawo gida ne kafin karshen makon nan kuma daga nan ne shugaban zai karrama su.
A wani labari makamancin wannan, ’yan wasan Najeriya da suka fafata a gasar daga karfe mai nauyi da ya gudana a yankin Asiya a garin Almaty da ke Kazakhstan suna samun nasara. Kawo yanzu tawagar ta lashe lambobin yabo 11 kuma sun kafa sabon tarihi har sau uku a wasanni daban-daban a gasar.