Buhari zai nada hadimarsa kwamishinar zabe

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai nada Mai Ba Shi Shawara na Musamman kan Shafukan Zumunta, Lauretta Onochie da wasu mutum uku a matsayin Kwamishinonin Hukumar Zabe na Kasa. A safiyar Talata, Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan ya karanta jerin sunayen da  Buhari ya aike wa Majasilar domin amincewa. Buhari da Osinbajo za su ci […]

Buhari zai nada hadimarsa kwamishinar zabe

Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai nada Mai Ba Shi Shawara na Musamman kan Shafukan Zumunta, Lauretta Onochie da wasu mutum uku a matsayin Kwamishinonin Hukumar Zabe na Kasa.

A safiyar Talata, Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan ya karanta jerin sunayen da  Buhari ya aike wa Majasilar domin amincewa.

Shugaban ya ce yin hakan shi ne abin da ya dace da kundin tsarin mulkin kas ana 1999.

Sauran wadanda shugaban ke neman nadawa kwamishinan zabe su ne Farfesa Mohammed Sani daga Jihar Katsina Katsina, Farfesa Kunle Ajayi daga Jihar Ekiti, sai kuma Sa’idu Ahmed daga Jihar Jigawa.

Karin bayani na tafe…