Buhari zai tafi Habasha ranar Lahadi

Ana sa ran dawowar Shugaban Kasar Abuja ranar Talata.

Buhari zai tafi Habasha ranar Lahadi

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari tafiya

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai tafi kasar Habasha ranar Lahadi domin bikin sake rantsar da Abiy Ahmed a matsayin Fira-Ministan kasar.

Kakakin shugan, Femi Adesina wanda ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa ranar Asabar ya ce Buhari zai bar Abuja ne ranar Lahadi gabanin bikin rantsuwar da za a yi ranar Litinin mai zuwa.

A cewar sanarwar, an sa ran shugaban ya yi jawabin fatan alheri, sannan ya halarci wata walima ta musamman a Fadar Gwamnatin kasar tare da sauran shugabannin kasashen da za su halarta.

Har lia yau, sanarwar ta ce yayin tafiyar, Buhari zai sami rakiyar Ministan Harkokin Waje na Najeriya, Geoffrey Onyeama da Shugaban Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NIA), Ambasada Ahmed Rufa’i Abubakar.

Ana sa ran dawowar Shugaban Kasar Abuja ranar Talata.

Abiy Ahmed da ya sake samun zama Fira-Ministan Habasha a karo na biyu bayan jam’iyyarsa ta yi galaba a zaben majalisar kasar da ya gudana a watan Yuni.

Tun da farko dai, Shugaba Buhari ya taya Abiy Ahmed murnar sake lashe zaben, inda ya tabbatar masa da cewa Najeriya za ta ci gaba da goyon bayan hadin kai da ’yancin kasar ta Habasha da ma sauran kasashen Afirka.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno