Buhari zai yi wa Najeriya aiki da kudin da yake kwatowa – Ya’u PJ
Garkuwar al’ummar Hausa/Fulani na karamar Hukumar Bassa a Jihar Filato, Alhaji Ya’u Bala PJ Jingir ya ce yana da tabbacin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, zai yi wa al’ummar Najeriya ayyukan rasa kasa da makudan kudin da gwamnatinsa take kwatowa daga manyan jami’an gwamnatin da ta gabata, wadanda suka sace a lokacin da suke mulki. Alhaji […]
Garkuwar al’ummar Hausa/Fulani na karamar Hukumar Bassa a Jihar Filato, Alhaji Ya’u Bala PJ Jingir ya ce yana da tabbacin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, zai yi wa al’ummar Najeriya ayyukan rasa kasa da makudan kudin da gwamnatinsa take kwatowa daga manyan jami’an gwamnatin da ta gabata, wadanda suka sace a lokacin da suke mulki.
Alhaji Ya’u Bala PJ ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Jos, inda ya ce ya yi imani cewa duk kudin da aka kwato daga barayin gwamnati, Shugaban kasa zai yi aiki da su, domin shi shugaba ne mai adalci.
“An dade ana sace kudin kasar nan, kuma an rasa yadda za ayi a kwato su, don haka ’yan Najeriya suka yi ta yin addu’a har Allah Ya kawo Shugaban kasa Muhammad Buhari. Don haka muna goyan bayansa kan wannan aiki da yake yi na kwato mana kudadenmu da aka sace,” inji shi.
Ya ce bincike ba zai hana wannan gwamnati aiki ba kamar yadda wasu suke fada, domin akwai hukumomin da aka dora wa kowane aiki. Ya ce mutanen da suka raba kudin da aka ware don sayo makaman da za a yaki ’yan Boko Haram, ko ba a tuhume su ba, Allah zai tambaye su.
Domin sun yi sanadin asara rayukan dubban mutane tare da dukiyoyi masu yawa. Ya ce da sun sayo makaman da abin bai yi muni haka ba, balle har a yi asarar rayuka sosai.
Ya yi kira ga ’yan Najeriya su kara yin hakuri da wannan gwamnati kuma su ci gaba da yi mata addu’a domin tana da kyawawan kudirori gare su.