Buhun masara 8 na fara nomawa amma yanzu ina noma buhu 8,000 – Kamilu Sigau
Alhaji Kamilu Sa’idu Sigau matashi ne da ya yi fice kan noman masara da wake a Karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna. A tattaunawa da wakilinmu, ya ce ya fara noma buhun masara takwas ne; amma yanzu yana noma masara sama da buhu 8,000: Mene ne tarihin rayuwarka kuma a wane lokaci ka fara […]
Alhaji Kamilu Sa’idu Sigau matashi ne da ya yi fice kan noman masara da wake a Karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna. A tattaunawa da wakilinmu, ya ce ya fara noma buhun masara takwas ne; amma yanzu yana noma masara sama da buhu 8,000:
Mene ne tarihin rayuwarka kuma a wane lokaci ka fara sana’ar noma?
To ni dai an haife ni ne a garin Sigau, Karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna. Kuma an haife ni a 1984, wato shekara 35 da suka gabata. Na yi makarantar firamare a garinmu Sigau daga nan na yi sakandare a Lere. Bayan na kammala na tafi Kwalejin Kimiyya da Sana’a ta Nuhu Bamalli da ke Zariya, na yi difloma a harshen Hausa. Sana’ar noma kuma na gaje ta ce a gidanmu. Na taso na ga iyayena suna yin ta, don haka tun ina karami na fara wannan sana’a. Amma gaskiya asalin noma na kaina, na fara ne a shekarar 2000. Kuma na fara ne da noman masara, inda na noma buhu takwas, a shekarar 2001 kuma na noma buhu 30.
Kafin in tafi Zariya makaranta, ba na noma masarar da ta wuce buhu 50, amma a shekarar 2005 na noma masara buhu 60. A shekarar 2007 kuma na noma buhu sama da 170, a shekarar 2008 na dada samun wasu gonaki na noma sama da buhu 400. Daga nan na zo ina hadawa da noman wake, lokacin da na fara noman wake ba na noma abin da ya wuce buhu 30. Amma a shekarar 2010 na noma masara buhu 600 wake kuma buhu 200.
Amma yanzu ina noma masara sama da buhu 8,000, wake kuma ina noma sama da buhu 1,000. Kuma dukkan wannan noma da nake yi, babu wanda ya taba ba ni ko Naira daya, a gwamnatance ko iri ko taki, babu wanda ya taba ba ni. Na taso na ga mahaifina Alhaji Sa’idu Sarkin Noma Sigau yana noma dubban buhunan masara; amma yanzu na fi shi noma. A takaice yanzu ni da kannena muna noma masara sama da buhu dubu 20.
Yaya fadi ko girma gonarka?
Gaskiya ba gona daya ba ce, ina da gonaki sun kai 20 wadanda nake nomawa. Ka san mu ba damuwa muka yi da auna gona a ce hekta kaza ko kaza ba. Akwai dai gonar da nake noma buhu 1500 da wadda nake noma buhu 1000 da mai 800 da mai 600 da sauransu hawa-hawa.
Kana daukar masu yi maka aikin noma kamar mutum nawa?
Gaskiya ba zan iya tuna yawan mutanen da suke yi mini aiki a gonakina ba. Ka ga dai, ina da taraktocin noma guda uku kuma ina da motar da take kaiwa da komowa a gonakina, kuma motoci kowace tana da direba da yaron mota. Bayan wannan ma’aikata a bangaren masu shuka, ina dibar yara almajirai duk ranar da za mu je shuka kamar 200 a gona daya. Masu noma kuma suna zuwa ne daga jihohin Katsina da Jigawa, nakan debi kamar mutum 150. Idan aka zo girbin masara ma, su dawo su yi. Kuma kamar ta bangaren taki, ina sanya taki kamar buhu 2,000 a gonakina duk shekara.
Ka ce ko gwamnati ba ta taba ba ka tallafi ba, koda na taki yaya aka yi haka?
Ban taba samun komai daga gwamnati ba a noman da nake yi. Amma an taba bai wa mahaifina taki a gwamnatin baya, wato lokacin gwamnatin PDP. Ka ga dai ni dan Jam’iyyar APC ne gaba da baya, amma a wannan gwamnati ban taba samun tallafin komai ba, a noman da nake yi. Amma kamar yadda na fada a lokacin PDP, zamanin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Alhaji Ahmed Muhammed Makarfi sun bai wa mahaifina sabuwar taraktar noma kuma lokacin ana sayar da motar kan Naira miliyan biyar, amma suka bai wa mahaifina kan Naira miliyan biyu. Kuma suka ce zai biya a cikin shekara uku. Sun ba shi taki buhu 150 zuwa 200 kan farashin gwamnati. Amma a wannan karo ko buhu daya mahaifina da ni ba mu samu ba. Amma a bara wani dan majalisa, ya aiko mini da buhun taki biyu.
Wadanne nasarori ka samu a noman da kake yi?
Gaskiya babu abin da zan ce wa harkar noma, sai dai in yi wa Allah godiya, domin duk wata harka da ka ga ina yi ta dalilin noma ne. Bayan aikin Hajji na farko da na je, wanda mahaifina ya biya mini na sake komawa a lokuta daban- daban. Kuma na je aikin Umarah da dama kuma na biya wa matana da kannena da kannen mahaifiyata aikin Hajji. Kuma ina gudanar da harkokin kasuwancin masara da taki kuma ina da gidaje da wuraren ajiye kaya da gidan mai da mutane suke cin abinci. Duk ta dalilin noma na samu wadannan abubuwa.
Wadanne matsaloli kake ganin suke damun manoma a wannan yanki?
Babbar matsalar manoma ita ce rashin farashin kayayyakin amfanin gona mai kyau. Saboda matsalar rashin farashi mai kyau za ka ga wani lokaci, idan manoma suka yi noma sukan yi hasara. Kamar noman da aka yi a bara, farkon kaka manoma sun sayar da buhun masara har Naira dubu biyar. Bayan lokacin noma sun kashe kudade wajen huda da noma kuma sun sanya taki sau daya ko sau biyu, an samce masarar an gyara ta, an sanya a buhu an dauko an kawo gida. Amma manomi ya zo ya sayar da buhu Naira dubu biyar. Ta yaya manomi zai mayar da kudin da ya kashe?. Ko mu da nomanmu ya habaka, ai bayan mun samu jari a noman ne, muka kama wasu harkoki daban.
Wane kira kake da shi zuwa ga gwamnati game da tallafa wa harkokin noma?
Ni babban rokona ga gwamnati kan harkokin noma shi ne gwamnati ta taimaki manoma da kayayyakin aikin noma irin na zamani musamman a wannan yanki na Saminaka. Wato kamar taraktocin noma da taki da inganta farashin kayayyakin amfanin gona.
Gwamnati ta taimaki manoman Najeriya ta daina bari ana shigo da kayayyakin amfanin gona daga waje. Don haka rufe kan iyakokin kasar nan da gwamnati ta yi alheri ne ga manoma da al’ummar kasar nan baki daya.
Domin farkon zuwan gwamnati Buhari da ta rufe kan iyakokin kasar nan, manoma da dama sun yi arziki a lokacin, saboda kayayyakin amfanin gona sun yi daraja. A lokacin da amfanin gona ya yi daraja, ana samun sama da mutum 600 da suke zuwa aikin Hajji a wannan yanki. Amma da amfani gona ya yi araha da kyar aka rika samun mutum 150. Aikin Hajjin bara mutanen da suka tafi daga wannan yanki, ba su wuce mutum 150 ba. Haka a bana ba su wuce mutum 170 ba, saboda matsalar rashin farashin amfanin gona. Idan amfanin gona ya yi daraja a bana, za ka ga komai ya canja, masu tafiya aikin Hajjin za su karu.
Don haka gwamnati ta dauki matakai kan matsalar rashin farashi mai kyau kan kayayyakin amfanin gona. Kuma ina bai wa gwamnati shawara ta fito da wani tsari na sayen kayayyakin amfanin gona daga hanun manoma tana ajiyewa. Lokacin da talakawa suka shiga matsalar rashin abinci, sai ta fito da shi ta sayar a kan farashi mai sauki. Ka ga an taimaki manomi shi kuma mutumin birni da ba ya noma, ma’aikaci ko dan kasuwa zai ji dadi.
Kamar yadda gwamnati take yi kan man fetur ta sayo da tsada ta sayar wa talakawa kan farashi mai rahusa. Wato gwamnati ta rika sanya tallafi a kayayyakin amfanin gona, kamar yadda take sanya tallafi kan man fetur. Idan gwamnati ta sanya tallafi kan kayayyakin amfanin gona, zai amfani manoma kuma zai amfani talakawan Najeriya baki daya. Yin haka zai dada sanya al’ummar Najeriya su rungumi aikin noma.