BUK ta dakatar da ɗaukar karatu saboda zanga-zanga

Jami’ar ta ɗauki matakin sakamakon yadda zanga-zangar ta rikiɗe zuwa tashe-tashen hankula.

BUK ta dakatar da ɗaukar karatu saboda zanga-zanga

Hukumar Gudanarwar Jami’ar Bayero ta Kano, ta sanar da dakatar da ɗaukar darusa zuwa wani lokaci, sakamakon zanga-zangar adawa da yunwa da ake ci gaba da yi a faɗin Najeriya.

Wata sanarwa da Jami’ar ta fitar ranar Litinin, ta ce ta ɗauki matakin ne bayan zama da ta yi da duba batun zanga-zangar da ake yi.

“Mun damu da lafiyar ɗalibai da kuma dukiyoyinsu, shi ya sa muka ɗauki matakin.

“Muna kira ga ɗalibai da ma’aikatanmu da su ci gaba da kula da irin zirga-zirgar da za su yi a wajen Jami’a domin kaucewa shiga hatsari.”

Jami’ar ta kuma shawarci ɗaliban da ke zaune a cikin makarantar da su kwantar da hankalinsu, sannan su kasance masu bin doka da oda.

Kazalika, Jami’ar ta bayar da tabbacin komawa ɗaukar darusa da zarar al’amura sun daidaita a jihar.

DSS ta kama ’yan Boko Haram 10 a Osun

Mutum 60 sun mutu a fashewar tankar mai a Neja

Solskjaer ya zama sabon kocin Besiktas

Nijeriya ta zama abokiyar hulɗar ƙungiyar BRICS