Bukatata in shahara a Kanyywood kamar yayata – Maryam Isa

Da farko za mu so ki gabatar da kanki ga masu karatu.Assalamu alaikum. Ni dai sunana Maryam Isa. An haife ni a birnin Kano, a unguwar Brigade. Na yi makarantar firamare a Gama Tudu, na yi sakandare ta kwana a ’Yargaya, inda na kammala a 2009. Ina ganin wannan shi ne tarihina a takaice.An ce […]

Bukatata in shahara a Kanyywood kamar yayata – Maryam Isa
Bukatata in shahara a Kanyywood kamar yayata – Maryam Isa

Da farko za mu so ki gabatar da kanki ga masu karatu.
Assalamu alaikum. Ni dai sunana Maryam Isa. An haife ni a birnin Kano, a unguwar Brigade. Na yi makarantar firamare a Gama Tudu, na yi sakandare ta kwana a ’Yargaya, inda na kammala a 2009. Ina ganin wannan shi ne tarihina a takaice.
An ce kina da alaka da Mansura Isa, ko yaya dangantakarku take da ita?
To ita dai Mansura Isa yayata ce, mahaifinmu daya da ita. Don haka ni kanwarta ce.

Yaya aka yi kika shiga harkar fim? Ko ita ce ta kawo ki?
E, gaskiya, daman ina da sha’awar harkar fim tun tuni, saboda yadda ake fadakarwa a cikinta kuma ita ma ’yar uwata zan iya cewa yanayin rawar da ta taka a harkar fim ya ja hankalina, saboda irin gudunmuwar da ta bayar. Ga shi ta bar fitowa a fim amma har yanzu ana tunawa da ita. To, yadda ta tafiyar da rayuwarta shi ne ya burge ni.

Yawancin wadanda suke shiga harkar fim suna zuwa da wani buri da suke son cin mawa, wani buri kike da shi a masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood?
Abin da ya kawo ni Kannywood shi ne don in ba da gudunmuwata wajen fadakar da al’umma, wajen wayar musu da kai dangane da wani abu da ya shige musu duhu. Na kuma shigo harkar fim ne don wa’azantarwa, nishadantarwa da kuma fa’idantar da al’umma.

A kalla yanzu kin samu tsawon wane lokaci a harkar fim?
To, gaskiya ban dade da farawa ba, don yanzu ban fi wata uku ba kuma kamar yadda na fada maka yadda muke da Mansura; ita ce ta karfafa mini gwiwa kuma take nuna mini yadda ya kamata na tafiyar da rayuwata a harkar fim.

Ga shi ba ki dade a harkar ba, amma har kin fara yin fina-finai kuma sunanki ya yadu a masana’antar fina-finan Hausa (Kannywood), to mene ne sirrin?
E, gaskiya kamar yadda na fada maka, ina bin tsarin yayata ne saboda na ga yadda ta zauna da kowa lafiya, ta samu karbuwa kuma ga shi tana nuna mini abin da ya kamata in yi. Don haka na dauki abin da muhimmanci; sai mutane suke kallo na a hakan.

To, yanzu ana ganin ki a wuraren daukar fim da yawa, kin fara fitowa a cikin wasu fina-finan ne?
E, na fito a fina-finai da dan dama zuwa yanzu, sai dai wasu ban san sunansu ba. Amma dai wadanda na sani a yanzu akwai Rai Da Rayuwa, akwai Turai, sai Aurena Rayuwata, da wani fim Rumaisa na kamfanin Ibrahim Bauni. Sai kuma ayyukan da ake kawo mini suna da dan dama.

Ganin yadda a dan karamin lokaci kika karbu haka, yaya kike jin kanki a wannan matsayi?
Babu abin da nake ji sai farin ciki, don haka kullum nake godiya ga Allah kuma ina fatan Allah Ya kara mini daukaka a harkar fim.

Ko kin fuskanci wata matsala da kika shigo harkar musamman a wuraren daukar fina-finai (lokeshin)?
Ka san abin da ka sa kanka ba ka ganin wahala kuma ita matsala duk wata harka ta rayuwa tana da tata matsalar.

Mansura ta kai ga babban matsayin da ta zarce sa’anninta a lokacinta ko ke ma kina da burin haka?
Ina da burin haka ni ma, domin babu wata ’yar fim da za ta zo ba ta yi fatan ta kai matsayin Mansura ba, domin kuwa jaruma ce da duniya ta san ta kuma ta yi ta gama ta tafi da mutuncinta. Don haka ina fatan ni ma in rike wannan matsayi.

Daga lokacin da kika shiga harkar fim zuwa yanzu, yaya mu’amalarki take da ’yan fim musamman mata?
Ina da mu’amala mai kyau da su, domin duk inda na hadu da su, ina kyautatata musu mu’amala, inda muke yin aiki mu gama, wato mu hadu lafiya, mu rabu lafiya.

Kina da kawaye ko wata aminiya a cikin ’yan fim?
Gaskiya ba ni da kowa, duk wata shawarata da ta shafi harkar fim da yayata nake yi, ita take tsara mini yadda zan yi, saboda haka ba ni da wata kawa da zan ce zan ja ta mu yi shawara, ’yar uwata ita ce komai.

Kin gamsu da yadda ake gudanar da harkar fim a yanzu?
E, gaskiya na gamsu duk da dai ni bakuwa ce a harkar amma yadda na ga ana gudanar da ita abin yana burge ni. Daraktoci suna yin kokari sosai wajen gudanar da aikinsu. Kuma su ma jarumai suna yin iyakar kokarinsu.

Mene ne sakonki ga ’yan kallo?
To, sakona na karshe ina kira ga masu kallo da su rika yi wa ’yan fim uzuri a game da fadakarwar da suke yi, domin idan dan fim ya fito a wani mugun matsayi sai ka ga ana ta zaginsa, ai ba halin mutum ba ne, fadakarwa ce, ’yan fim suna da hali mai kyau.