Bukukuwan Kirsimet i: Shugabanni sun bukaci ’yan Najeriya su zauna lafiya da juna

A yayin da Kiristoci a Najeriya suka bi sahun akwarorinsu na duniya wajen gudanar da bukukuwan Kirsimeti a jiya da yau Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan da Shugaban Majalisar Dattawa da ta Wakilai Aminu Waziri Tambuwal sun bukaci ’yan Najeriya su sadaukar da kawunansu wajen kyautata wa juna tare da tabbatar da zaman lafiya da […]

Bukukuwan Kirsimet i: Shugabanni sun bukaci ’yan Najeriya su zauna lafiya da juna
Bukukuwan Kirsimet i: Shugabanni sun bukaci ’yan Najeriya su zauna lafiya da juna

A yayin da Kiristoci a Najeriya suka bi sahun akwarorinsu na duniya wajen gudanar da bukukuwan Kirsimeti a jiya da yau Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan da Shugaban Majalisar Dattawa da ta Wakilai Aminu Waziri Tambuwal sun bukaci ’yan Najeriya su sadaukar da kawunansu wajen kyautata wa juna tare da tabbatar da zaman lafiya da lumana da nuna hakuri da kyawawan dabi’u a lokacin da suke mu’amala a tsakaninsu.
A sakonsa Shugaba Jonathan ya bukaci Kiristoci da ’yan Najeriya su gode wa Allah kan yadda cikin rahamarSa Ya taimaka Najeriya ta tsallake matsaloli da dama.
Shugaba Jonathan ya ce gwamnatinsa za ta yi duk abin da za ta iya domin tabbatar da cewa idan wakilan jama’a suka taru a babban taron kasa a badi sun samu dama da karfafa abin da zai tabbatar da hadin kai don ci gaban zaman lafiyar kasar nan da hadin kanta.
Ya ce “Da taimakon Allah gwamnatina za ta ci gaba da aiwatar da shirinta na sake fasalin kasa domin ci gaba da cika alkawarin da ta yi na inganta rayuwar daukacin ’yan Najeriya.”
Shi kuwa Sanata Dabid Mark kira ya yi ga ’yan Najeriya su yi amfani da bambance-bambancen siyasa da na kabila da addini wajen fifita hadin kan kasa. Ya yi kira ga manyan ’yan siyasa su nuna misali nagari wajen tabbatar da zaman lafiya da bin doka da oda, inda ya yi gargadin cewa bai kamata a sarayar da bukatun kasa saboda bukatun son kai na daidaiku ko rukunin mutane ba.
Ya ce, “Kullum muna cewa kalubalen da ke gabanmu suna da yawa, to amma tilas ne mu gane babu wanda zai zo daga sama ya magance mana matsalolinmu.”
A nasa sakon dauke da sanya hannun kakakinsa Malam Imam Imam, Shugaban Majalisar Tarayya Aminu Tambuwal ya bukaci ’yan Najeriya su ci gaba da nuna halaye nagari da za su dinke kasar nan tare da karfafa harkokin mulki da inganta zaman lafiya.
Tambuwal ya bukaci mabiya addinai su ci gaba da gudanar da addu’o’in zaman lafiya da kawanciyar hankali da hadin kan kasa, tare da bukatar mabiya addinan su kasance masu taimakon juna kuma su guji munanan dabi’u da ayyukan da za su jawo tarnaki ga yunkurin da gwamnati ke yin a samar da ribar dimokuradiyya ga jama’a.