Bukukuwan Mauludi: Kiristoci sun shirya bikin maulidi ga Musulmi a Kaduna

A wani yankuri na karfafa fahimtar juna a tsakanin Musulmi da Kiristoci, wata kungiyar Kiristoci a Jihar Kaduna mai suna Gidauniyar Farfado da Zaman Lafiya da Sulhuntawa (Peace Rebibal and Reconciliation Foundation), a karkashin jagorancin Fasto Yohanna Buru ta shirya bikin Mauludi ga al’ummar Musulmi, domin tunawa da ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammadu (SAW).Shugaban […]

Bukukuwan Mauludi: Kiristoci sun shirya bikin maulidi ga Musulmi a Kaduna

????????????????????????????????????

A wani yankuri na karfafa fahimtar juna a tsakanin Musulmi da Kiristoci, wata kungiyar Kiristoci a Jihar Kaduna mai suna Gidauniyar Farfado da Zaman Lafiya da Sulhuntawa (Peace Rebibal and Reconciliation Foundation), a karkashin jagorancin Fasto Yohanna Buru ta shirya bikin Mauludi ga al’ummar Musulmi, domin tunawa da ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammadu (SAW).
Shugaban kungiyar, Fasto Yohanna Buru ya ce sun shirya bikin ne domin taya Musulmi bikin Maulidi don samar da hadin kai a tsakanin Musulmi da Kirista a jihar.
Fasto Buru ya ce lokaci ya yi da Musulmi da Kirista za su gane cewa tushen addininsu shi ne tsoron Allah. “Babu Musulmin kwarai ko Kiristan kwarai da ya yi imani da addininsa da zai yarda da zaluntar dan uwansa mutum saboda kawai addininsu ba daya ba.  Wannan rabuwar kawuna a tsakanin Musulmi da Kiristoci ta samo asali ne saboda ’yan siyasa da ke yin shishigi a addinai kuma suke samun taimakon wasu malamai da fastoci,” inji shi.
Fasto Buru ya bayyana shirin da suke yi domin fadada wannan manufa ta kungiyarsu, inda ya ce nan gaba za su shiga kasashen Ghana da Togo da Benin da Chadi domin shirya tarurrukan wayar da kan Musulmi da Kiristoci domin su kara yarda da juna a yayin gudanar da al’amuransu.
A jawabin Sheikh Salisu Maibarota, cewa ya yi duk wanda ya taya Musulmi murna a wannan rana ya nuna cewa ba addininsa kawai yake mutuntawa ba har da addinin wasu. Ya ce “Al’ummar Musulmi sun yi imani da Annabi Isa a matsayin daya daga cikin manyan Annabawan Allah, hakan ya sa idan aka zagaya gidajen Musulmi za a ji ’ya’yansu na amsa sunan Isa.”
Daga Kano, Lubabatu I. Garba,  ta ruwaito mana cewa mabiya Shi’a sun bi sawun sauran Musulmin duniya wajen gudanar da bikin mauludi a ranar Talatar, inda maza da mata da yara suka yi fitar dango suka zagaya birnin Kano suna wakokin yabon Manzon Allah (SAW).
Ta ce mabiya Shi’ar sun taru ne a Babban Masallacin Kano kafin su nufi titin Mandawari zuwa
Jakara zuwa Kwanar Dala zuwa Gwammaja zuwa kofar Mazugal inda suka tsaya Masallacin Juma’a na Fagge inda malamai suka gudanar da jawabai.
Shugaban kungiyar Malam Mahmud Turi, ya yi bayani kan muhimmancin mauludi ga al’ummar Musulmi inda ya ce ranar na tunatar da al’ummar Musulmi game da zuwan Manzon Allah (SAW) wanda ya sauya duniya daga duhu zuwa haske kuma daga jahilci zuwa ilimi daga zalunci zuwa adalci.
Ya jawo hankalin Musulmi kan hadin kai da mugun sakamakon da rarrabuwa ke kawowa. “Ba wani abu ne ya jefa al’ummar Musulmi a cikin mummunan halin wulakanci da kaskanci a Iraki da Afganistan da Yaman da Siriya da Falasdinu da Pakistan da Somaliya da Afirka ta Tsakiya da makamantansu ba, illa rarrabuwar kai.  Sannan mawuyacin halin da muke ciki na danniya da zalunci da rashin tsaro da rudu a Najeriya sakamako ne na yin watsi da sakon Manzon Allah (SAW),” inji shi.
Daga Minna, Muhammad danladi Ibrahim ya ce fiye da makarantun Islamiyya da kungiyoyin Musulmi 800 daga sassan Jihar Neja ne suka yi jerin gwano daga Babban Masallacin Minna a karkashin jagorancin kungiyar Majma’u Ihayi Zikra Maulidi Nabiyyi. Ya ce manya da yara sun hadu tun misalin karfe 8:00 na safe aka yi zagayen har zuwa 5:00 na yamma.
Shugaban kungiyar Malam Muhammad Isah Kutigi, ya ce makasudin bikin shi ne tunatar da jama’a wasu daga cikin dabi’un Annabi (SAW) wanda Allah Ya ce aiko shi rahama ne ga duniya. Malam Isah ya ce, ya kamata al’ummar Musulmi su yi nazarin hanyoyin tunkarar al’amuran da suke ci wa addini da kasar nan tuwo a kwarya da suka hada da matsalar tsaro da tattalin arziki don kubutar da kasar nan.
Babban Limamin Minna Sheikh Ibrahim Isah Fari, ya ce sakaci da koyarwar Annabi ne ya jefa Musulmi cikin halin da suka samu kansu, inda ya shawarci Musulmi su rika koya wa ’ya’yansu karatun Alkur’ani da addini da cusa musu kaunar Annabi Muhammad (SAW) da iyalan gidansa.
Gwamnan Jihar Neja, Dokta Mu’azu Babangida Aliyu wanda Malam Aliyu Garafini ya wakilta, ya yi kira ga al’ummar Musulmi ne su ci gaba da koyi da halayen Annabi (SAW) da suka hada da zaman lafiya da juna, domin kawar da matsalar tashin hankali da ta tattalin arziki da ake fuskanta a yanzu.