Bukukuwan Sallah: Shugabanni sun bukaci a zauna lafiya

A sakonninsu na ga al’ummar Musulmi kan shagulgulan karamar Sallah ta bana, shugabanni sun yi kira ga jama’ar Najeriya su ci gaba da zaman lafiya da lumana a tsakaninsu, kuma su kara hakuri kan halin da ake ciki domin gwamnati tana da kudirin gyara ne ga al’umma.A sakonsa na Sallah Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya […]

Bukukuwan Sallah: Shugabanni sun bukaci a zauna lafiya

A sakonninsu na ga al’ummar Musulmi kan shagulgulan karamar Sallah ta bana, shugabanni sun yi kira ga jama’ar Najeriya su ci gaba da zaman lafiya da lumana a tsakaninsu, kuma su kara hakuri kan halin da ake ciki domin gwamnati tana da kudirin gyara ne ga al’umma.
A sakonsa na Sallah Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci al’umma su kara yi wa gwamnatinsa hakuri kan halin da suka tsinci kansu sakamakon tabarbarewar tattalin arziki. Shugaba Buhari ya ce yana da masaniya game da matsin da ’yan Najeriya suke ciki kuma ya yi alkawarin cewa, nan gaba za a ji dadi a kasar nan.
A sakon Ministan Birnin Tarayya, Abuja, Malam Muhammad Musa Bello, ya hori Musulmin birnin ne su ci gaba da addu’a ga kasa a yayin shagulgulan karamar Sallar. Ministan ya taya Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan lafiya kuma ya bukaci Musulmi su ci gaba da aiki da koyarwar da suka samu a cikin watan na Ramadan.
A sakon tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar, cewa ya yi a kara hakuri da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari kuma a yi ta yi masa addu’ar alheri da samun nasara.
Atiku Abubakar, ya ce Shugaba Muhammadu Buhari na sane da matsatsin da ake ciki, kuma ya ce idan mutane suka kara hakuri lallai za su mori ribar dimokuradiya. “Ya kamata a jinjina wa Shugaba Buhari saboda kokarin da yake yi domin hana handama da babakere da kudin jama’a ta yadda babu dama a juyar da kudin da za a yi mutane aiki zuwa aljihun wasu daidaikun mutane.
Shi ma Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki ya bukaci Musulmi ne su ci gaba da nuna halayen kirki da suka koya a cikin watan Ramadan.  Saraki a sakonsa na barka da Sallah, ya bukaci ’yan Najeriya su jajirce kuma su yi addu’a kan yanayin da tattalin arzikin kasa ke ciki. “Idan muka yi hakuri muka yi aiki na kwarai kamar yadda Allah Ya ce, to lallai za mu fita daga cikin wannan matsala da muke ciki,” inji Saraki. Ya kara da cewa idan har muna so mu dawo da mutuncinmu, to, dole ne mu yi hakuri da juna, mu zauna lafiya da juna kuma mu bi doka da oda. “Ina kira ga ’yan Boko Haram da sauran masu ta da zaune-tsaye a kasar nan su canja ra’ayi su zauna lafiya albarkacin karamar Sallah.
Daga Sakkwato wakilinmu Nasiru Bello, ya ruwaito Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar yana cewa lokaci ya yi da Musulmin duniya za su hadu domin sanin dalilan da suka sanya harkar ta’addanci ke kara wanzuwa a kasashensu wanda ba haka lamarin yake a kasashen da ba na Musulmi ba. Sarkin Musulmi ya bayyana haka ne a sakonsa na Sallah, inda ya ce duk inda rashin zaman lafiya da ta da zaune-tsaye da kashe mutane ya yi kaka-gida a duniyar za a samu na Musulmi ne, me ke kawo haka? Me ya sa sai a wurinmu alhali addininmu bai yarda da tashin hankali da ta’addanci ba?  Ya kamata shugabannin Musulmi na duniya su hadu don magance ta’adancin.
Sarkin Musulmi ya yi tir da tsinuwa ga wadanda suka kai hari a kusa ga masallacin Manzon Allah (SAW) a Madina, “Kuma za mu roki Allah Ya tona asirinsu domin a hukunta su yadda lamarin ta’adanci zai bar kasashen Musulmi gaba daya,” inji shi.
Ya yi godiya ga malaman Musulunci da suka gudanar da tafsirin azumin bana bisa ga karantarwar da suka yi mai kyau da inganci ba zagi ko batanci. Sai ya yi kira ga jama’a kan su mara wa shirin Gwamnatin Tarayya na farfado da harkar noma baya wajen tashi tukuru su yi noma su nome fili komai kankantarsa don mara wa Shugaba Buhari baya a shirinsa na wadata kasa da abinci.
Shi kuwa Gwamnan Jihar Nasarawa Umaru Tanko Al-Makura ya yi kira ga Musulmin su yi amfani da kyawawan halayen da suka koya a cikin watan Ramadan domin zai taimaka wurin hadin kan al’ummar kasa baki daya.
Gwamna Almakura wanda ya bayyana haka a sakonsa na Salllah dauke da sanya hannun kakakinsa Ahmed Tukur, ya ce yana sa ran Najeriya za ta amfana sosai da koyarwar Ramadan. Ya ce “Idan aka yi hakuri aka yi addu’a kuma aka ci gaba da jin tsoron Allah, to lallai Najeriya za ta dunkule wuri daya kuma a yi aiki tare wurin ciyar da kasar nan gaba. Al-Makura ya bukaci ’yan Najeriya su zama masu son juna da girmama juna.
Daga Maiduguri wakilinmu Tijjani Usman Bello, ya ce sakamakon samun zaman lafiya da kwanciyar hankalin da Jihar Borno ta fara samu bayan fama da yakin Boko Haram na tsawon shekara bakwai a karon farko gwamnatin jihar ta janye hana zirga-zirgar ababen hawa tun daga ranar karamar Sallah a garin Maiduguri da kewaye.
Gwamnan Jihar Alhaji Kashim Shettima, ya sanar da haka a garin Maiduguri, bayan kammala taron masu ruwa da tsaki a kan harkar tsaro, don duba yanayin yadda za a gudanar da bikin Sallar na bana.
 Janye takaita zirga-zirgar ya haifar da jin dadi da farin ciki ga jama’ar jihar kan yadda suka gudanar da sallarsu cikin jin dadi da annashuwa.
Wani mazaunin Maiduguri, Malam Bukar Ali, ya ce, “Wannan dage dokar zirga-zirgar ta zo min a daidai domin kuwa na kai tsawon shekara biyar ina gudanar da bikin Sallah a gida babu shagulgula kamar ba Sallah ba, kuma babu ziyarar ’yan uwa da abokan arziki, babu hawan Sallah. To amma a bana jami’an tsaro sun sakar mana mara za mu gudanar da bukuwan Sallarmu cikin annashuwa tare da ziyartar ’yan uwa da abokan arziki. Wallahi ina gode wa gwamnati da jami’an tsaro da suka yi ta maza suka kawo mana karshen wannan bala’in na Boko Haram duk da cewar ba a kawo karshe ba, to amma na yi imanin an karya lagonsu.” Ita kuwa wata matashiya mai suna Malama Halima, ta ce “dage dokar hana zirga-zirga a ranar Sallah ya sa ni fitowa a yau Sallah domin in ziyarci ’yan uwa da abokan arziki kuma ka ga yanzu na wuce gidan kallo ne don in bai wa idona abinci. Ke nan na san cewa yau take Sallah ba kamar da ba muna gida ba mu san ana Sallah ba, gwamnati da jami’an tsaro sun kyauta mana a wannan lokaci na bukukwan karamar Sallah.”
Daga Gombe wakilinmu Rabilu Abubakar ya ce shekara bakwai ba a yi Hawan Sallah a Gombe ba, sai  bana, inda a bara ma rashin tsaro ya hana a gudanar da Sallar Idi a Masallacin Idi, sai a Babban Masallacin kofar Fadar Sarki aka yi sakamakon tashin wani bama-bamai a kasuwar Gombe ana gobe Sallah. Ya ce a bana Masallacin Idin ya yi cikar kwari yayin gudanar da sallar da babban Limamin Gombe Alhaji Muhammad Pindiga ya jagoranta.
A hudubarsa Limamin ya ja hankalin mutane ne su rika kyautata sallolin nan biyar dakyautata rayuwa tare da cika mudu ga ’yan kasuwa. Alhaji Pindiga, ya ce duk Musulmi na kwarai ya dace ya kyautata imaninsa ya kasance yana ibada sosai koda bayan Ramadan ne.
A jawabin Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Ibrahim Hassan dankwambo ga al’ummar jihar ya hore su ne da su koma gona domin samar wa kasa abinci. Gwamna dankwambo, ya kuma yi kira ga jama’ar jihar su daina zuba shara a magudanun ruwa domin kauce wa aukuwar ambaliya a wannan lokaci na damina.
An gudanar da Hawan Sallah a kofar fadar Sarkin Gombe bayan da aka shafe shekara bakwai ba a yi ba saboda rashin tsaro, inda aka yi hawan dawakai sosai da ya burge jama’a da suka jima ba su ga haka ba.
A jawabin Mai martaba Sarkin Gombe Alhaji Abubakar Shehu Abubakar, ya gode wa Allah ne da Ya ba shi ikon yin hawan da kuma yadda aka yi Sallah lafiya ba tare da samu rahoton wani tashin hankali ba. Kuma ya gode wa jama’ar Gombe kan hadin kai da goyon baya da suke ba shi a dukkan wasu al’amura da suka shafi ci gaban jihar.
Hawan Sallar ya samu halartar manyan baki na ciki da wajen jihar da suka hada da tsohon Mukaddashin Gwamnan Jihar Taraba Alhaji Garba Umar UTC da tsohon Kakakin PDP na kasa Farfesa Rufa’i Ahmad Alkali da Garkuwan Gombe Sanata Sa’idu Umar Kumo da sauran manyan ’ya’yan jihar.
Daga Zariya wakilinmu Aliyu Babankarfi ya ce bikin Sallar bana ya kayatar sakamakon samun zaman lafiya, inda aka gudanar da bikin karamar Sallah cike da annasuwa da kayatarwa tare da gudanar da bukukuwan Hawan Sallah da Mai martaba Sarkin zazzau Alhaji Shehu Idris ya yi da hakimansa, inda Sarki ya hau doki daga masallacin Idi zuwa fadarsa, daga nan hakimai suka gabatar da gaisuwar Sallah gare shi.
A jiya Alhamis kuma an gudanar da Hawan Bariki inda Sarkin zai yi hawa ya ziyarci gidan gwamnati domin kai gaisuwa ga Gwamna tare da bayyana masa halin da masarautarsa ke ciki. Sai kuma yau da ake sa ran Sarkin ya yi Hawan Daushe da zai zagaya gari yana gayar da ke al’ummarsa su kuma su yi jerin gwano suna yi masa gaisuwa, bayan ya sauka dukkan hakimansa za su gabatar da gaisuwa da jinjina a wani biki mai kayatarwa. Wannan hawa yana samun halartar baki daga sassan duniya kuma a hawan ne ake zaben hakimin da ya fi kowane hakimin iya hawa da bajinta, a karshe kuma Sarkin ya gabatar da jawabi.
 Daga Kafanchan, wakilinmu Ahmed Ali ya ruwaito Mai martaba Sarkin Jama’a Alhaji Muhammad Isa Muhammad ne yana yaba da matakan samar da zaman lafiya da Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i ke dauka wanda hakan ya taimaka wajen samun kwanciyar hankali da ci gaban jihar.
Sarkin, wanda ya gabatar da jawabin Sallah a kofar fadarsa jim kadan da saukowa daga Sallar Idi, ya nuna godiya ga Shugaban karamar Jukumar Jama’a da jami’an tsaro da dukkan jama’ar da suke taimaka wa masarautarsa, inda ya yi fatan Allah Ya karbi ibadun da al’ummar Musulmi suka gudanar a watan Ramadan kuma ya yi addu’ar zaman lafiya da ci gaban jiha da kasa baki daya.