Bullar cutar amai da gudawa ta kashe mutum 5 a Gombe
Hukumomin jihar Gombe sun sanar da sabuwar bullar cutar amai da gudawa inda cutar ta yi sanadiyyar rasuwar mutum biyar yayin da wasu kimanin 16 suke jinya a cibiyar kiwon lafiya na Kembu da ke karamar hukumar Balanga a jihar. Mukaddashshin shugaban hukumar dakile cututtuka na jihar Dakta Nuhu Bile ne ya bayyana wa kamfanin […]
Hukumomin jihar Gombe sun sanar da sabuwar bullar cutar amai da gudawa inda cutar ta yi sanadiyyar rasuwar mutum biyar yayin da wasu kimanin 16 suke jinya a cibiyar kiwon lafiya na Kembu da ke karamar hukumar Balanga a jihar.
Mukaddashshin shugaban hukumar dakile cututtuka na jihar Dakta Nuhu Bile ne ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na NAN a Gombe.
Bile ya ce, cutar ta barke ne a watan Oktoban. A yanzu haka sun sallami majinyata 70 daga asibitoci bayan kamuwa da cutar, yayin da biyar suka rasu.