Bullar cutar Kurona a Legas ta firgita mu amma – Mazauna Legas da Ogun

A ranar Juma’ar makon jiya ne Najeriya ta tabbatar da bullar cutar Kurona a Jihar Legas bayan da wani dan kasar Italiya da ke aiki da kamfanin siminti na Lafarge da ke Ewekoro a Jihar Ogun ya shigo da ita. Dan Italiyan wanda kwantar da shi a wani asibiti da ke kamfanin kafin a kai […]

Bullar cutar Kurona a Legas ta firgita mu amma – Mazauna Legas da Ogun

A ranar Juma’ar makon jiya ne Najeriya ta tabbatar da bullar cutar Kurona a Jihar Legas bayan da wani dan kasar Italiya da ke aiki da kamfanin siminti na Lafarge da ke Ewekoro a Jihar Ogun ya shigo da ita. Dan Italiyan wanda kwantar da shi a wani asibiti da ke kamfanin kafin a kai shi Legas, zuwa yanzu ya sa an rufe kamfanin simintin tare da killace mutum 28 da suka yi mu’amala da shi. Kuma gwamnonin jihohin Legas da Ogun sun bada sanarwar neman mutum 100 da suka yi mu’amala da shi.

Aminiya ta zanta da wadansu mazauna jihohin biyu domin jin yadda suka ji game da bullar cutar, inda Malam Usman Ibrahim Tunau dan jarida da ke zaune a Unguwar Obalande a Legas ya ce ba abin mamaki ba ne cutar ta bulla a Legas lura da yawan jama’a da suke zuwa daga kasashen duniya daban-daban. “Kuma ka ga Legas birni ne da yake matsayin zango ga masu tafiya a jiragen sama daga kasashe da dama, don haka komai na iya faruwa,” inji shi

Ya ce mutane da dama sun kadu sun shiga tashin hankali domin a yanzu haka abin rufe hanci ya yi karanci a kasuwa haka man wanke hannu,”Mutane suna cikin zullumi sosai, sai dai babu wani abu da ya sauya kawo yanzu domin ana gudanar da harkoki a wuraren ayyuka da kasuwa kamar yadda aka saba,” inji shi.

Shi kuwa Muhammadu Tukur Ibrahim da ke zaune a garin Agege kuma yake harkokin kasuwanci a cikin Legas ya shaida wa Aminiya cewa, “Mun samu labarin bular cutar Kurona a Legas amma muna gudanar da al’amuranmu yadda suka kamata sai dai ana samun sauye-sauye kamar a masallacin Juma’a na sojin sama da muka yi sallah a makon jiya, duk wanda zai shiga sai ya wanke hannunsa da omo sannan ya sake daurayewa kafin ya shiga masallacin.  Hukumar masallacin ta tanadi kayayyakin wanke hannuwa  na musamman, haka ofishin Hukumar Shige da Fici da ke PWD, su ma kafin ka shiga akwai sabulu da detol da ruwa sai ka wanke hannunka ka goge kafin ka shiga.”

Malam Rabi’u Auwal Dan’azumi mazaunin garin Idi Araba cewa ya yi, “Hakika ba mu ji dadi ba kuma mun shiga firgici da jin wannan labari, to amma tunda abin ya bullo babu abin da za mu yi sai kokarin daukar matakan kariya daga wannan annoba.”

Ya ce akwai sakacin hukuma a lamarin har mutumin ya shigo ya fita daga tashar jirgin sama ba tare da an duba lafiyarsa ba har ya tafi wata jihar sannan aka gane yana dauke da cutar, “A sauran kasashe ba haka abin yake ba, duk sa’ar da wani bako ya zo daga kasar da aka san akwai wannan annoba ana tsananta bincike a kansa,” inji shi.

Malam Musa Yahaya Muhammad Nice cewa ya yi, “Da farko dole hankalina ya tashi saboda tunanin yanayin da mai karamin karfi ke shiga idan ciwo ya same shi na rashin samun kula a kan lokaci daga asibitocinmu, amma yanzu alhamdulillah da irin gudunmawra da wadansu daga cikin likitoci suke bayarwa kan hanyoyin samun kariya daga cutar. Kuma babban abin sha’awa shi ne mutane sun maida al’amarinsu ga Allah wajen dukufa da addu’ar neman kariya. Yanzu dai mu a Jihar Legas har mun fara maida lamarin a matsayin tarihi, don ba ma tunanin yaduwar cutar.”

Baffa Ramalan jami’i ne da ke koyarwa a Makarantar Sarrafa Jiragen Ruwa ta Costal Maritime da ke Legas cewa ya yi abu mafi mahimmanci shi ne a maida hankali wajen bin matakan kariya da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta zayyana da na Cibiyar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Kasa. Ya ce tsabta da yin amfani da kayayyakin kariya da kula da shiga taron jama’a, da nesa da masu zazzabin da ke da alaka da mura, domin cuta ce da ke da yanayi na mura mai zafi wacce da ke tushe kafofin numfashi.

A Jihar Ogun, Muhammed Dunama likitan dabobbi da ke aiki a Jami’ar Gona ta Tarayya (FUNAB) da ke Abeokuta, ya shaida wa Aminiya cewa rashin sani ne ya sanya mutane ke rububin sayen kyalle kariya na hanci da baki lamarin da ya sanya farashinsu ya yi tashin gwaron zabo kuma suka yi karanci a kasuwa. Ya ce wadanda suka kamu da cutar Kurona ne ke bukatar amfani da kyallen fuskar domin gudun kada su yada ta, “Amma wanda bai kamu ba zai iya amfani da matakin kariya na wanke hannuwa da kaurace wa wajen da ake zaton cutar ta yadu, ko sabulu ko omo mutum ya wanke hannunsa da shi a-kai-a-kai ya wadatar,” inji shi.

Lawal Abdullahi Matazu da ke zaune a garin Ogere a Jihar Ogun cewa ya yi ba su ji dadin bullar cutar a Legas da Ogun ba, sai dai da yake yin Allah ne babu abin da bawa zai iya sai addu’a da daukar matakan kariya. “Tabbas abu in ya zo Legas a Nahiyar Afirka matukar ba a yi taka- tsantsan ba, zai iya yin illa sosai, lura da yawan jama’a,” inji shi.