Bullar zazzabin Lassa ta halaka mutum biyu a jihar Kogi

Kwamishinan lafiya na jihar Kogi, Dakta Haruna Saka, a yau Alhamis ya tabbatar da rasuwar mutum biyu sanadiyyar bullar cutar zazzabin Lassa wanda aka gano a farkon wannan shekarar. Maiba Gwamnan Kogi shawara ta musamman Dakta Ahmed Attah, wanda ya wakilci Kwamishinan ya bayyanawa manema labarai hakan a Lokoja babban birnin jihar Kogi lokacin da […]

Bullar zazzabin Lassa ta halaka mutum biyu a jihar Kogi

Kwamishinan lafiya na jihar Kogi, Dakta Haruna Saka, a yau Alhamis ya tabbatar da rasuwar mutum biyu sanadiyyar bullar cutar zazzabin Lassa wanda aka gano a farkon wannan shekarar.

Maiba Gwamnan Kogi shawara ta musamman Dakta Ahmed Attah, wanda ya wakilci Kwamishinan ya bayyanawa manema labarai hakan a Lokoja babban birnin jihar Kogi lokacin da yake bayani game  da yaduwar cututtuka a jihar.

Dakta Ahmed, ya ce a wannan shekarar sun samu rahoton bulllar cutar Lassa da ta kama mutum 10. An samu bullar cutar ne a kananan hukumomin Ibaji da Ijumu