Buni ya amince da N70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi
Gwamnan ya ce sabon albashin zai fara aiki daga watan Disamban 2024.
Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya amince da Naira 70,000 matsayin mafi ƙarancin albashin ma’aikatan jihar, wanda zai fara aiki daga watan Disamban 2024.
Wannan ya biyo bayan shawarwarin da kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa ya bayar kan sabon tsarin albashin.
- Sarkin Beli ya rasu bayan shafe shekara 91 a kan mulki
- 6 cikin kowane dalabai mata 10 an ci zarafinsu a jami’o’i 12 —Rahoto
Kwamitin ya kuma bayar da shawarar gyara yadda ake raba kuɗaɗen ƙananan hukumomin jihar, domin tabbatar da cewa sabon tsarin albashin ya fara aiki a dukkanin ƙananan hukumomin jihar.
Ana sa ran kammala shirye-shiryen da ake yi nan ba da jimawa ba, don tabbatar da cewa ma’aikatan ƙananan hukumomin jihar su ma sun fara samun sabon albashin.
Gwamnatin jihar ta buƙaci ma’aikata su ƙara dagewa wajen yin ayyukansu, domin nuna godiyarsu ta hanyar inganta ayyukan da aka ɗora musu.