Buni ya dakatar da shugaban ƙaramar hukuma kan rashin ɗa’a

Gwamnan ya dakatar da shugaban ne kan aikata rashin ɗa’a.

Buni ya dakatar da shugaban ƙaramar hukuma kan rashin ɗa’a

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya dakatar da shugaban ƙaramar hukumar Machina, Idrissa Mai Bukar, kan aikata rashin ɗa’a.

Gwamnan ya dakatar da shi na tsawon mako uku bayan an rantsar da shi da wasu 16 da aka yi biyo bayan lashe zaɓen ƙananan hukumomin jihar.

Dakatarwar na cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan jihar, Shu’aibu Abdullahi, ya fitar.

Abdullahi, ya ce Gwamna Buni ya yi amfani da sashe na 2 na dokar ƙaramar hukuma ta 2019 wajen dakatar da shugaban saboda aikata rashin ɗa’a.

Buni, ya umarci shugaban da aka dakatar da ya miƙa al’amuran ƙaramar hukumar ga mataimakinsa zuwa lokacin da dakatarwar za ta kammala aiki.