Buni ya dawo da Sakataren APC da su Gwamnan Neja suka kora
Sanata Akpandeodehe tare da Mai Mala Buni sun bayyana tsigewar a matsayin shaci fadi
Rikicin shugabannin jam’iyyar APC ya yi wata sabuwar juyi, inda Sakataren Kwamitin Riko da Shirya Babban Taron Jam’iyyar na Kasa, Sanata John James Akpandeodehe, wanda aka dakatar ya ci gaba da aiki a hedikwatar jam’iyyar.
Sanata Akpandeodehe wanda aka ba da rahoton dakatarwa ta wata takarda da mambobin kwamitin, in banda shugaban rikon jam’iyyar, Mai Mala Buni, ya ci gaba da aiki ne bayan dawowar Buni daga kasar waje.
- Buni ya yi ganawar sirri da kwamitin babban taron APC
- Yadda mazan Afirka ke shigar matan Larabawa domin shiga Dubai
Tuni Buni ya fara jagorantar kwamitin wajen sasanta jagororin jam’iyyar da ke wa juna kallon hadarin kaji gabanin babban taron, wanda jam’iyyar ke so a samu nasarar gudanarwa cikin lumana da hadin kai a yayin da take shirin fara tunkarar babban zaben 2023.
A ranar Juma’a, washegarin dawowar Buni daga kasar waje, shi da Akpandeodehe suka bayyana a hedikwatar jam’iyyar domin ci gaba da shirye-shiryen babban taron; Sun bayyana batun tsige sakataren daga kujerarsa a matsayin labarin kanzon kurege.
A zantawarsa da ’yan jarida, Sanata Akpandeodehehe ya ce shi ne halastaccen sakataren jam’iyyar, bisa umarnin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na cewa a bar abubuwa a yadda suke a jam’iyyar, ba tare da wani sauyi ba.
Takardar dakatar da Sakataren na APC ta fito ne dai a lokacin jagorancin Mukaddashin Shugaban Kwamitin Rikon Jam’iyyar, Gwamna Abubakar Sani Bello na Jihar Neja, bisa zargin rashin iya tafiyar da aiki.
Dambarwar tafiyar da jam’iyyar bayan tafiyar Buni ganin likita a kasar waje ta dauki zafi ne bayan Gwamna Bello ya bayyana cewa shi ne Buni ya nada a matsayin mukaddashi — wanda hakan ya jawo ce-ce-ku-ce da zargin korar Buni, abin da wadansu suka kira da juyin mulki.
Kafin nan dai Sakataren Jam’iyyar shi ne ke gudanar da harkokin kwamitin rikon a duk lokacin da Buni ba ya nan.
“Buni ba zai taba saba umarnin shugaban kasa ba, wanda a wasikarsa ta karshe ya ba da umarnin a bar abubuwa a yadda suke; Buni mutum ne mai basira da ya san kimar shugaban kasa kuma ba zai saba umarninsa ba.
“Har yanzu ni ne Sakataren Jam’iyyar APC kuma kundin tsarin mulki ya fayyace komai a game da haka. Sannan INEC ta ce ba za a iya sallamar mutum ba, sai an ba da wa’adin akalla kwana 21.
“Ya kamata a jinjina min saboda tsayawata kai da fata tare da Shugaban Rikon Jam’iyyar, duba da irin biyayya da nagarta da na nuna.
“Me ya za a hukunta ni saboda na tsaya tare da shi? Dattaku ke nan. Saboda haka babu wani abu da aka sauya a APC. Ni ne sakatarenta kuma ana ci gaba da sasanta bangarori. Jam’iyya daya ce,” inji shi.
A halin yanzu dai Buni na jagorantar kwamitin riko da babban taron jam’iyya wajen sasanta jagororin jam’iyyar da ke wa juna kallon hadarin kaji gabanin babban taron.
Wannan wani kokari ne na gabin babban taron ya gudana ba tare da hatsaniya ba, cikin hadin kai da nasara a yayin da jam’iyyar ke shirin fara tunkarar babban zaben 2023.