Buni ya shirya bikin karrama daliban da suka lashe gasar duniya
Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, ya shirya gagarumin bikin karrama daliban jihar Nafisa Abdullah ’yar shekara 17 da Rukayya Muhammad Fema ’yar shekara 15, bayan sun lashe gasar duniya da aka kammala da kasar Birtaniya.
Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, ya shirya gagarumin bikin karrama daliban jihar Nafisa Abdullah ’yar shekara 17 da Rukayya Muhammad Fema ’yar shekara 15, bayan sun lashe gasar duniya da aka kammala da kasar Birtaniya.
Nafisa ta lashe Gashar Iya Turanci ta Duniya a yayin da Rukayya ta lashe Gasar Muhawar ta duniya, inda suka doke kasashe 69 a Gasar TeenEagle na shekarar 2025 da aka gudanar a birnin Landan.
Bayan doke dalibai sama da 20,000 da suka fafata a gasar inda suka wakilci Najeriya daga Kwalejin Nigerian Tulip (NTIC) da ke Jihar Yobe.
Nafisa da Rukayya dukkansu sun ci gajiyar shirin tallafin karatu na Gwamna Mai Mala Buni wanda ya kunshi cikakken dawainiyar karatun dalibai 890 a NTIC.
- An soka wa jami’in Sibil Difens wuka har lahira a Jigawa
- Nafisa ta cancaci kyautar Dala 100,000 da gida da OON —Pantami
Gwamna Buni ya bayyana wannan nasara da ’yan matan suka samu a matsayin babban abin alfahari ga jiha da kuma Najeriya baki daya.
“Wadannan manyan ayyuka ne da ke sa mu yi alfahari da kuma tabbatar da saka hannun jarin gwamnati a fannin ilimi,” in ji Gwamna Buni.
Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da bayar da tallafin karatu ga kowane yaro a jihar domin samun damar zuwa makaranta, ya kuma yi qira ga iyaye da su ba su haxin kai.
A halin yanzu, akwai kimanin daliban jihar Yobe 40,000 da ke samun tallafin karatu na gwamnati da ke karatun kwasa-kwasai daban-daban a jami’o’i da sauran manyan makarantu a Najeriya da kasashen ketare.
Idan dai ba a manta ba a ’yan watannin da suka gabata jihar ta yi bikin yaye dalibai 167 da suka ci gajiyar shirin tallafin karatu da jihar ta samu wadanda suka kammala karatunsu a fannin likitanci da kwamfuta da kimiyyar injiniyanci daga jami’o’in kasar Indiya.