Bunkasa Ilimi: Yadda aka koya wa marubuta wallafa littafi da Manhajar Bloom
Burin kowane marubuci shi ne ya ga an wallafa abin da ya rubuta cikin littafi kuma sakonsa ya watsu a ko’ina cikin duniya, ta yadda al’umma za su karu, su ilimantu, su fadaka, sannan kuma su nishadantu. Sai dai a halin da ake ciki, musamman a kasashe masu tasowa na Afrika, marubuta na fuskantar matsaloli […]
Burin kowane marubuci shi ne ya ga an wallafa abin da ya rubuta cikin littafi kuma sakonsa ya watsu a ko’ina cikin duniya, ta yadda al’umma za su karu, su ilimantu, su fadaka, sannan kuma su nishadantu.
Sai dai a halin da ake ciki, musamman a kasashe masu tasowa na Afrika, marubuta na fuskantar matsaloli da dama, musamman dangane da isar da sakonninsu ta hanya mai sauki. Dalili ke nan kungiyoyin bunkasa ilimi na ADEA (The Association for the Debelopment of Education in Africa) da GBA (Global Book Alliance) da USAID (United States Agency for International Debelopment) suka dauki nauyin koyar da marubuta fasahar wallafa littattafansu cikin hanya mai sauki ta amfani da sabuwar Manhajar Bloom.
A wannan yunkuri na wadannan kungiyoyi da cibiyoyi na bunkasa ilimi da samar da littattafai cikin harsunan duniya ga al’ummma, sun shirya wani kwarya-kwaryan kwas na kwana hudu ga wasu zababbun marubuta guda tara da suka fito daga kasashen Najeriya, Ghana, Kamaru da Kenya. Kwas din ya ta’allaka ne da wata sabuwar manhajar kwamfuta mai suna Bloom, wacce ta hanyarta marubuci zai iya wallafa littafinsa da ma na wasu cikin harsunan duniya da suka hada da Ingilishi, Faransanci, Larabci, Hausa, Ibo, Yoruba, Ashante, Fulfulde da sauran harsuna fitattu da ake iya rubutawa.
Kwas din, wanda aka gudanar a otel din Chelsea da ke Abuja daga ranar 17 zuwa 20 na Afrilun bana, ya gudana ne a karkashin koyarwar wani kwararren masanin manhajar ta Bloom, mai suna Dokta Paul S. Frank da ke aiki a Amurka.
Yayin kwarya-kwaryan bikin bude kwas din, wanda ya gudana a zauren taro na Chelsea Hotel Abuja, wakiliyar Ministan Ilimi na Najeriya, Darakta a Ma’aikatar Ilimi ta Najeriya, Dokta Chioma C.J Nwadei ta bayyana farin cikin ma’aikatar ilimi ta Najeriya, yadda cibiyoyin bunkasa ilimi na ADEA, GBA da USAID suka zabi gudanar da kwas din a Najeriya.
“Abin yabawa ne da godiya, yadda kuka zabi Najeriya da marubutan Najeriya wajen kawo sauyi da bunkasa ilimi ta hanya samar da littattafai da yada su a Afrika da Asiya da ma duniya baki daya, wanda haka zai saukaka koyo da koyarwa,” inji ta.
Kasancewar kwas din na koyi ka koyar ne, Ma’aikatar Ilimi ta Najeriya ta nuna shirinta na karfafa wa marubutan da suka halarci kwas din wajen bunkasa abin da suka koya ga sauran marubutan Najeriya, ta yadda za a yi amfani da wannan manhaja ta Bloom wajen yada ilimi ta hanyar amfani da harsunan gida.
A nata bangaren, wakiliyar cibiyar USAID a Najeriya, Madam Croshelle Harris Hussein ta bayyana dalilin da ya sanya cbiyar tasu ta tallafa wajen gudanar da wannan kwas. Ta ce sun yi la’akari ne da muhimmancin wannan mahnaja ta Bloom, wacce ta fasaharta, marubuta za su yi amfani da ita wajen yada ilimi ga al’umma, musamman wajen amfani da harsunan gida domin tsara littattafan da za su ilimantar ga musamman yara.
“daya daga cikin burin wannan kwas shi ne, ya samar da littattafai masu dauke da darussan karfafa gwiwa ga yara da matasa, wadanda za su cusa kishin kasa, burin gina kasa da haifar da zaman lafiya tsakanin al’umma,” a cewarta.
“Haka kuma, yana cikin kudurin Cibiyar USAID ta yi amfani da wannan dama wajen bunkasa koyo da koyarwa cikin harsunan gida, kamar kuma yadda hakan zai kara farfadowa da bunkasa dabi’ar karatu a cikin al’umma.”
Dangane da haka, jami’ar ta USAID ta ce suna nan suna yin shirin hadin gwiwa da Jami’ar Bayero Kano domin bunkasa rubuce-rubuce cikin harshen Hausa, wanda haka zai samar da littattafan karatu, musamman domin yada ilimi cikin al’umma.
Shi ma Shugaban kungiyar Marubuta ta Najeriya (ANA), Mista Denja Abdullahi, wanda ya halarci bikin bude kwas din, ya bayyana jin dadinsa da aka samar da wannan manhaja kuma aka zabi marubutan Najeriya su kasance cikin masu koyon yadda ake amfani da ita wajen wallafa littafi.
Ya bayyana cewa, wannan manhaja ta Bloom da kuma yunkurin cibiyoyi da kungiyoyin da suka dauki nauyin wannan kwas, zai bunkasa ilimi ba ma a Najeriya da sauran nahiyoyin Afrika ba, a’a a dukkkan fadin duniya.
Baya ga Denja Abdullahi, shi ma tsohon Shugaban kungiyar Marubuta ta Najeriya kuma wanda ke tallafa wa harkar rubutu da marubuta, Dokta Wale Okediran, ya halarci bikin bude kwas din, inda a dan takaitaccen jawabinsa ya yi murna da samar da wannan mahnaja, sannan ya gode wa cibiyoyin da suka dauki nauyin koya wa marubuta yadda ake amfani da ita.
Marubuta ’yan Najeriya da suka samu halartar kwas din sun hada da Bashir Yahuza Malumfashi, Khalid Imam, Isyaku Bala Ibrahim, Bilkisu Yusuf Ali da Amina Hassan Abdulsalam. Sauran sun hada da Madam Claris Ujam da Anthonia Opara da Olarike Adesanya da Ugwu Kenneth Gibson.
Daga kasar Kamaru kuwa, Mista Eyo Aku ne ya samu halarta, sai kuma Mista Ebans Mensah da Mista Kwadwo Osei da suka halarta daga kasar Ghana.
A wata takardar bayani da ta shigo hannun wakilinmu, an bayyana dalla-dalla manufofi da kudurorin wadannan kungiyoyin sa-kai da suka dauki nauyin shirya wannan kwas na manhajar wallafa littattafai ta Bloom. ADEA, kungiya ce mai zaman kanta, wacce ke ayyukan da suka shafi bunkasa ilimi a nahiyar Afrika. A yayin gudanar da ayyukanta, kungiyar tana hada hannu da cibiyoyi da hukumomin ilimi na nahiyar Afrika da kungiyoyin jinkai na duniya. Tana da rassa a kasashe daban-daban na Afrika.
GBA, cibiya ce mai zaman kanta ita ma, wacce take gudanar da ayyukanta a sassa daban-daban na duniya. Tana hada hannu da cibiyoyi da hukumomi da kungiyoyin sa-kai wajen samarwa da rarraba littattafai da kayayyakin koyo da koyar da ilimi a kasashe masu tasowa na sassan duniya.
Game da USAID kuwa, ita cibiya ce ta Majalisar dinkin Duniya, wacce ke tallafa wa kasashen duniya ta fannoni daban-daban na rayuwa, da suka hada da bunkasa ilimi da sauransu.
Madam Lily Nyariki, ita ce ta kasance jami’ar tafiyar da kungiyar ADEA a kasar Kenya. Ita ce ta shirya wannan kwas, inda ta nemi hadin gwiwar kungiyoyin GBA da USAID tare da sahalewar Ma’aikatar Ilimi ta Najeriya domin gudanar da kwas din a Abuja Najeriya.
“Za mu ci gaba da hulda da Ma’aikatar Ilimi ta Najeriya domin ganin mun ci gaba da shirya kwasa-kwasai da suka danganci bunkasa ilimi a Najeriya ta amfani da harsunan gida,” inji Madam Lily, wacce ta zo daga kasar Kenya tare da abokin aikinta Mista Roberts.
A yayin bikin kammala kwas din a ranar Jumu’ar da ta gabata, inda aka rarraba wa dukkan mahalarta takardun shaida, jagoran koyar da kwas din, Mista Paul S. Frank ya yi godiya sosai ga marubutan da suka halarci kwas din, sannan ya yaba da yadda suka maida hankali har aka samu kammalawa cikin fahimtar juna.