Buratai da sauransu su sauka, inji Majalisa

Hafsoshin tsaron Najeriya su sauka kawai tunda kashe-kashen karuwa yake yi.

Buratai da sauransu su sauka, inji Majalisa

Manyan Hafsoshin Tsaron Najeriya a Fadar Shugaban Kasa

Majalissar Dattawa ta bukaci manyan hafsoshin tsaron Najeriya su yi murabus tunda kullum kashe-kashen da ake yi a kasar karuwa yake yi.

Hakan ya biyo bayan kudirin da Sanata Ali Ndume (APC, Borno) ya gabatar a zauren Majalisar a ranar Talata, kan ritayar da sojoji fiye da 200 ke so su yi don kashin kansu a tsakanin nan.

‘Yan majalisar ta kuma bukaci kwamitin hadakar majalisar kan harkokin tsaro ya binciko dalilan da ke sa sojojin suke yin murabus.

A jawabinsa, Shugaban Majalissr Dattawa, Ahmad Lawan, ya ce jami’an tsaron suna iya kokarinsu, amma sai sun kara kaimi.