‘Yan bindiga: Sojoji sun bude sansani a Faskari

Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta bude babban sansani domin yakar ayyukan ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane a yankin Faskari na Jihar Katsina. Yayin kaddamar da sansanin, Babban Hafsan Rundunar, Laftanar Janar Tukur Buratai ya ce sansanin zai mayar da hankali ne wajen yakar ‘yan bindiga da dangoginsu da ke addabar al’ummomin yakin […]

‘Yan bindiga: Sojoji sun bude sansani a Faskari

Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta bude babban sansani domin yakar ayyukan ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane a yankin Faskari na Jihar Katsina.

Yayin kaddamar da sansanin, Babban Hafsan Rundunar, Laftanar Janar Tukur Buratai ya ce sansanin zai mayar da hankali ne wajen yakar ‘yan bindiga da dangoginsu da ke addabar al’ummomin yakin Arewa-maso-Gabas.

“Za a kaddamar da yyukan dauki a daukacin sassan kasar nan guda shida a tare domin kyautata alaka tsakanin sojoji da fararen hula”, kamar yadda ya ce.

Ya ce sansanin da ire-irensa a sauran yankunan na daga abubuwan da aka tsara na bikin Ranar Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya na bana (NADCEL 2020) wanda ya kunshi fara aikin soji na musamman, ‘Exercise Sahel Sanity’, domin nuna karfin rundunar na yakar miyagun laifuda a fadin Najeriya.

Sai dai ya ce bikin na bana bai hada da bangaren tunawa da ‘yan mazan jiya ba saboda cutar coronavirus, amma za a yi kyakkyawan tanadin yin sa bayan lafawar cutar.

Janar din sojin ya kuma musanta zargin da ake wa sojoji na kin kai dauki a kan kari, da kuma shigowar dakarun Jamhuriyar Nijar cikin Najeriya, yana mai cewa a daina siyasantar da al’amarin tsaron Najeriya.

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50