Buratai ya bukaci sojoji su gaggauta murkushe ’yan ta’addanci
Buratai ya kara kira a gare su da su kokarta su muttsike matsalar, kar ta samu gindin zama kamar yadda aka gani a kasashen Sri Lanka da Columbia.
Tsohon Babban Hafsah Sojin Kasan Najeriya, Tukur Yusuf Buratai, ya yi kira ga shugabannin soji sun hanyarta kawo karshen ayyukan ta’addanci a yankin Tafkin Chadi.
Laftanar-Janar Buratai mai ritaya ya yi wannan kira ne a Taron Kasa da Kasa na Farko da Sashen Binciken Tarihi da Dabaru na Jami’ar Maiduguri ya gudanar a Jihar Borno.
Da yake jinjina wa sojoji da sauran jami’an tsaro bisa kokarinsu da yadda suke sayar da rayukansu wajen murkushe kungiyoyin ta’addanci, Buratai ya kara kira a gare su da su kokarta su muttsike matsalar, kar ta samu gindin zama kamar yadda aka gani a kasashen Sri Lanka da Columbia.
“Muna ganin ya kamata a kammala yakin nan da lokaci, kar a bari ya tsawaita kamar na kasashen Columbia da Sri Lanka,” in ji Buratai.
- Jiragen dakon kaya tsakanin Najeriya da Saudiyya za su dawo aiki —Keyamo
- NAJERIYA A YAU: Yadda Za Ku Kauce Wa Cututtukan Masu Yaduwa Da Damina
- ’Yan acaɓa sun kai hari ofishin ’yan sanda a Legas
Ya jaddada muhimmancin hadin kai tsakanin sojoji da sauran hukumomin tsaro wajen dakile ayyukan laifi da samar da tsaron rayuka da dukiyoyi.
Da haka ne a cewarsa, cikin wata biyar sojoji suka yi nasarar kwace kananan hukumomi tara daga hannun ’yan ta’adda a Jihar Borno a zamanin jagorancinsa.
A jawabinsa, Shugaban Jami’ar Maiduguri, Farfesa Aliyu Shugaba, ya ce jami’ar ba ta ba da kai bori ya hau ba wajen dakatar da harkokinta, duk kuwa da hare-haren kunar bakin wake hudu da kungiyar Boko Haram ta kai jami’ar.