Burin ciyar da al’umma gaba ya sa nake takarar Majalisar Tarayya-Dan Dagazau
Aliyu Inuwa Dan Dagazau ya bayyana cewa yana son tsayawa takara ne domin cika burinsa na ciyar da al’ummarsa gaba. Aliyu Inuwa Dan Dagazau matashi ne mai taimakon al’umma kuma mai kishin ganin ci gaban al’umma musamma Mata da Matasa da marasa karfi wanda tun kafin shigar sa siyasa yake taimakawa irin wadannan mutane har […]

Aliyu Inuwa Dan Dagazau ya bayyana cewa yana son tsayawa takara ne domin cika burinsa na ciyar da al’ummarsa gaba.
Aliyu Inuwa Dan Dagazau matashi ne mai taimakon al’umma kuma mai kishin ganin ci gaban al’umma musamma Mata da Matasa da marasa karfi wanda tun kafin shigar sa siyasa yake taimakawa irin wadannan mutane har yanzu ya yanke sha’awarar tsayawa takarar kujerar Majalisar Dattawa ta tarayya don ganin ya ciyar al’ummar sa gaba.
Aliyu Inuwa Dan Dagazau yana takarar ne a jam’iyyar Social Democratic Party SDP domin wakiltar yankin Gombe da Kwami da Funakaye na jihar Gombe, sannan ya ce idan ya ci zabe zai bunkasa al’umma ta hanyar Noma da kuma ganin yadda za’a inganta harkar ilimi dan a yaki jahilci.
Dan Dagazau ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Gombe bayan da ya mayar da fom dinsa na tarakara a helkwatar sakatariyar jam’iyyar ta su ta SDP na kasa dake Abuja.
Ya ce kasancewarsa wanda ya san shiga da fita na yadda ake gudanar da harkar mulki zai yi iya kokarin sa wajen ganin duk abunda zai yi na ciyar da yankin Gombe da Kwami da Funakaye gaba ya yi dan su shaida ribar mulkin democradiyya a sanadiyar sa.
Har ila yau ya kuma tabbatar da cewa muddin al’ummarsa suka zabe shi ba zai bari su kasa shaida ribar romon mulkin siyasa ba domin shi a siyasa ba sabon yankar rake bane dan haka yake mai kiran su da su zabe shi domin shi ne dan takarar da jama’a za suyi alfahari da zaben sa ba
za su yi dana sani ba.
Aliyu Inuwa Dandagazau, yace shi dan siyasa ne da bai son ganin matasa suna zaman banza dan haka suma zai samar da shiri na musamman do min su mata kuma zai sa a koya musu sana’oin hannu ya basu jari a tallafa musu gajiyayyu kuma zai duba yadda zai bullo da tsarin da zai taimaka musu dan su dinga samun abunda za su gudanar da rayuwar su.
Daga nan sai ya yi amfani da wannan damar inda ya yi kira ga jama’a da kowa da kowa da su fito ranar zabe su zabi jam’iyyar SDP domin idan ta kafa gwamnati a matakai daban daban za’a yi walwala.