Burin ciyar da al’umma gaba ya sa nake takarar Sanata – dan Dagazau
Aliyu Inuwa dan Dagazau ya ce ya yanke shawarar tsayawa takarar Majalisar Dattawa ce don ciyar da al’ummar mazabarsa ta Gombe da Kwami da Funakaye a Jihar Gombe gaba tare da bunkasa al’umma ta hanyar noma da kuma ganin yadda za a inganta harkar ilimi don a yaki jahilci. Aliyu Inuwa dan Dagazau wanda ke […]
Aliyu Inuwa dan Dagazau ya ce ya yanke shawarar tsayawa takarar Majalisar Dattawa ce don ciyar da al’ummar mazabarsa ta Gombe da Kwami da Funakaye a Jihar Gombe gaba tare da bunkasa al’umma ta hanyar noma da kuma ganin yadda za a inganta harkar ilimi don a yaki jahilci.
Aliyu Inuwa dan Dagazau wanda ke takarar a Jam’iyyar SDP, ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Gombe bayan ya mayar da fom dinsa na takara a Sakatariyar SDP ta kasa da ke Abuja.
Ya ce kasancewarsa wanda ya san shiga da fitar yadda ake gudanar da harkar mulki zai yi iya kokarinsa wajen ganin duk abin da zai yi na ciyar da yankin Gombe da Kwami da Funakaye gaba ya yi, don su shaida ribar dimokuradiyya a sanadiyarsa.
Har ila yau ya tabbatar da cewa shi a siyasa ba sabon yankar rake ba ne, don haka yake kiran al’ummar yankin su zabe shi domin shi ne dan takarar da jama’a za su yi alfahari da zabensa ba za su yi da-na-sani ba.
Daga nan sai ya yi kira ga jama’a su fito ranar zabe su zabi SDP domin idan ta kafa gwamnati a matakai daban-daban za a yi walwala.