‘Burin farfado da al’adun Arewa ya sa muka kafa kungiyar wasan kwaikwayo a Legas’

Al’umma ’yan Arewa mazauna Kudancin Najeriya sun kafa kungiyar shirya fina-finan Hausa a Jihar Legas.kungiyar mai suna Gidan Tsuntsu Mobie, an kafa ta ne domin shirya wasannin kwaikwayo a Kurmi, maimakon dogaro kacokan da fina-finan Hausa da akan shirya a Arewa. Shugaban kungiyar, Ahmad Ibrahim dambatta ya shaida wa Aminiya cewa sun kafa kungiyar ne […]

‘Burin farfado da al’adun Arewa ya sa muka kafa kungiyar wasan kwaikwayo a Legas’
‘Burin farfado da al’adun Arewa ya sa muka kafa kungiyar wasan kwaikwayo a Legas’

Al’umma ’yan Arewa mazauna Kudancin Najeriya sun kafa kungiyar shirya fina-finan Hausa a Jihar Legas.
kungiyar mai suna Gidan Tsuntsu Mobie, an kafa ta ne domin shirya wasannin kwaikwayo a Kurmi, maimakon dogaro kacokan da fina-finan Hausa da akan shirya a Arewa.
Shugaban kungiyar, Ahmad Ibrahim dambatta ya shaida wa Aminiya cewa sun kafa kungiyar ne domin farfado da al’adun gargajiya a tsakanin ’yan Arewa mazauna Kurmi, domin a cewarsa babu iren-iren wannan kungiyar a baya.
Ya bayyana cewa kungiyar za ta fara shirya fina-finan Hausa da suka kunshi kyawawan hanyoyin nishadantarwa tare da kayatarwa da soyyaya, wadanda ba su saba wa al’adunmu da addinanmu ba, wadanda za su daga martabar al’adunmu na gargajiya a Kurmi da ma kasa baki daya.
Mataimakin shugaban kungiyar Yahaya Idris, wanda manaja ne a kamfanin MIKANO a bangaren sufuri ya shaida wa Aminiya cewa sun shirya tsaf don ganin kungiyar ta cin ma manufarta, domin ba da jimawa ba shi da abokinsa Sani suka saya wa kungiyar kyamara ta Naira dubu 300 kuma baya ga rejistar da shugaban kungiyar ya yi wa kungiyar a mataki na kasa sun kuma dauki lauya; wanda zai zayyana musu kundin da za su bi, domin kauce wa saba doka a aikin kungiyar.
Ya kuma yaba da kokarin ’yan kungiyar, ganin cewa a yanzu su ne ke gudanar da harkokinta da kansu da dukiyarsu, kafin Allah Ya sa su kai ga gaci.