Burin Gidauniyar MALLPAI tallafa wa mata da marayu – A’isha Bagudu

Hajiya A’isha Atiku Bagudu, Uwargidan Gwamnan Jihar Kebbi, ita ce Shugabar Gidauniyar MALLPAI. A tattaunawarta da wakilinmu, ta bayyana asalin gidauniyar da kuma kudurorinta. Ga yadda tattaunawar ta kasance: Tun yaushe ne kika kirkiro wannan Gidauniya taki kuma mece ce alkiblarta?Mun faro wannan gidauniya ce tun daga shekarar 2009, domin a shekarar ce aka yi […]

Burin Gidauniyar MALLPAI tallafa wa mata da marayu – A’isha Bagudu
Burin Gidauniyar MALLPAI tallafa wa mata da marayu – A’isha Bagudu

Hajiya A’isha Atiku Bagudu, Uwargidan Gwamnan Jihar Kebbi, ita ce Shugabar Gidauniyar MALLPAI. A tattaunawarta da wakilinmu, ta bayyana asalin gidauniyar da kuma kudurorinta. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Tun yaushe ne kika kirkiro wannan Gidauniya taki kuma mece ce alkiblarta?
Mun faro wannan gidauniya ce tun daga shekarar 2009, domin a shekarar ce aka yi mata rijista. Na ji dadi da ka yi mini wannan tambaya saboda mutane da yawa suna tunanin muna daukar wannan gidauniyar tamu a kan siyasa. To abin da ya kamata mutane su lura shi ne, mun fara gudanar da ita tun 2009, wato tun kafin shi maigidana ma ya fara fitowa batun takarar Sanata balle ma yau da Allah Ya ba shi mukamin gwamna.
Maganar alkibla kuwa, wannan gidauniya tamu, mun fuskantar da ita ne wajen taimakon al’umma, musamman ma mata da yara masu rauni, kamar marayu, marasa galihu, almajirai, nakasassu da makamantansu. Idan ka lura mu nan Arewa, akasari matanmu ba su yin sana’o’i, za ka ga sun rike hannu har sai mijinsu ya kawo musu, maimakon a da can inda za ka ga mata suna yin kananan sana’o’i, wadanda ta hanyarsu za ka ga suna huce wa kansu takaici kuma suna tallafa wa iyalinsu. Musamman za ka ga suna sayar da kamar kuli-kuli, gishiri, barkono da sauran irinsu.
A yanzu zamani ya canja, akwai bukatar mata su samu abin yi. Zan ba da misali da ni kaina da iyayena. Akwai lokacin da mahaifina yake aiki a kamfanin New Nigerian, aka dakatar da su daga aiki na tsawon kusan watanni shida ba su da albashi. Ina ganin mahaifiyarmu tana kulla kankara, muna taya ta. Lokacin ana kulla Tree Top a leda, mu sa a firij ya yi sanyi, a yi fanke ana sayarwa. Ga shi dai mahaifinmu bai da albashi amma ba mu rasa abinci ba, kuma lokacin ni ina makarantar sakandare ta kwana, wato Capital School Sakkwato, a lokacin. Amma da kudin wannan sana’a ake zuba mai a mota a kai mu makarantar, kuma da shi ake saya mana dukkan abin da muke bukata na kayan tafiya makaranta. Tun daga lokacin nan na gane tasiri da muhimmancin sana’a ga mace. Hakika ta hanyar sana’ar mace, za ta tallafa wa ’ya’yanta da mijinta a lokacin da bukatar haka ta taso, balle ma a wannan zamani mai wuyar sha’ani da muke ciki. Kuma babu mahaifiyar da za ta so a ce yau ga danta ko diyarta suna yawo a titi.
Game da batun tallafa wa mata da gidauniyarku take yi, shin bashin kudi ne kuke ba su, kyauta kuke ba su ko kuwa kuna koya musu sana’o’i ne?
Muna yin duka. A da muna bayar da kyauta ne amma sai muka lura da cewa wasu idan an ba su sai su je su sayar. Sai muka dauki cewa duk wanda ya ci gajiyar tallafin, kowane wata za ta ba da wani kason kudi haka, wadanda ba su taka kara suka karya ba, yadda dai za ta samu kulawar ci gaba da sana’ar. Zan ba ka misali da wata mace da ta zo neman tallafi, mijinta ya rasu, suna gidan haya kuma ga shi ba su da abin da za su yi, ga shi kuma an kore su daga gidan da suke hayar. Kan haka muka ba ta sharudda cewa za mu biya mata hayar kuma za mu ba ta jalin da za ta kama sana’a kuma ta tabbatar ta rike sana’ar kuma ’ya’yanta su kasance suna makaranta. Amma duk wata za ta rika kawo Naira dari biyar. Haka wasu daga cikin mutane suka rika mamakin cewa dari biyar ta yi kadan amma na mance da batunsu. Wannan hikima ta sanya matar nan ta rike sana’ar kuma ta samu ci gaba, sai ga shi da kanta ta zo tana rokon cewa za ta rika biyan Naira dubu daya maimakon dari biyar. A takaice dai sana’arta ta bunkasa kuma ta samu albarka har ta ce ta sayi fili za ta fara gini, domin barin gidan haya. To ka ga wannan nasara ce ni a wajena, wato tallafa wa rayuwar al’umma.
Idan muka koma baya, sunan wannan gidauniya taku MALLPAI, shin mene ma’anarta?
Mutane da yawa suna yi mani wannan tambayar, abin da MALLPAI ke nufi shi ne, Massa Literacy for the Less Pribilleged and Almajiri Initiatibe, (Gidauniyar Wayar da Kan Raunana da Almajirai). Mun ga sunan ya yi tsawo, don haka don a samu saukin sai muka takaita sunan da haruffa.
Ke nan ayyukanku sun hada da fadakarwa, ilimantarwa da sauransu?
kwarai da gaske kuwa, domin a yanzu haka muna da wani almajiri da ya kammala makaranta har ya fara aiki kuma gidauniyarmu ce ta dauki nauyin karatun nasa. Sannan kuma a yanzu haka akwai wasu almajiran da muke da su a Polytechnic a Birnin Kebbi, wasu kuma suna makarantun sakandare, wasu kuma a firamare. Kuma ba almajirai kadai ba, har da marayu maza da manta, muna daukar nauyin karatunsu. Wani abu da mutane ba su gane ba shi ne, ba yara maza kadai ke bara ba, akwai yara mata almajirai, wadanda su ma ake kai su karatu kuma suna bara. Akwai wani kauye da ba zan kira maka sunansa ba, an samu mata almajirai uku sun tsinci abinci a bola, suka ci, ashe akwai maganin bera a ciki. Dukkansu haka suka mutu. Akwai fyade da ake wa yara mata, kullum muna samun labarin haka. Don haka aikin gidauniyarmu ce fadakar da al’umma musamman mata yadda za a samu wayewar kai da ilimi domin ci gaban al’umma.
Ga kuma kukan da ake yi na yadda ake tura yara mata talla, ko me gidauniyarku take yi a wannan janibi?
Gidauniyramu na fadakarwa game da illolin tallace-tallace ga yara mata. Misali, akwai taro da muka kira a Jihar Kebbi na matan ’yan majalisa da kuma matan shugabannin kananan hukumomi. Mun yi magana da su game da tsaftace muhalli, game da talla da kuma magana game da yadda ake tura yara almajirci. A yanzu haka muna yawo kananan hukumomi, inda muke magana a bangarorin mata, muna tallafa musu da irin abin da za mu iya. Muna fadakar da al’umma don su gane tasirin hadin kai da taimakon juna, domin a daina raja’a kan gwamnati. A yanzu sai ka ga mutane kowa ya nade hannunsa yana jiran sai gwamnati ta yi masa komai, wanda wannan lokacin ya wuce. Don haka MALLPAI tana hada kai da kungiyoyin jama’a na Jihar Kebbi wajen gudanar da ayyukan tallafa wa al’umma.