Burin sabuwar gasar rubutu ta bunkasa adabin Hausa – Farfesa Ibrahim Malumfashi (2)

Mun ji tarihin samuwar gasa a kasar Hausa. To mene ne makasudin ita wannan gasa da Makarantar Malam Bambadiyya da Pleasant Library suka ta fito da ita? Kamar yadda muka gani, duk lokacin da aka gudanar da gasa ta rubutu abubuwa uku ke bayyana. Na farko za a sa wa jama’a shaukin son karanta abin […]

Burin sabuwar gasar rubutu ta bunkasa adabin Hausa – Farfesa Ibrahim Malumfashi (2)

Mun ji tarihin samuwar gasa a kasar Hausa. To mene ne makasudin ita wannan gasa da Makarantar Malam Bambadiyya da Pleasant Library suka ta fito da ita?

Kamar yadda muka gani, duk lokacin da aka gudanar da gasa ta rubutu abubuwa uku ke bayyana. Na farko za a sa wa jama’a shaukin son karanta abin da gasar ta samar, ma’ana, mutane za su zaku su ga gwanintar da aka tsara, wannan na kara yawaitar masu karatu. Na biyu, gasa na samar da sababbin abin karantawa da marubuta. Na uku, gasa na kara yayata muhimmancin adabi da rubutu a idon al’umma. Bisa irin wannan tunani ne Makarantar Malam Bambadiya da aka assasa a Intanet a shafin Facebook ta ga ya dace a sake sa azama ga marubuta domin su shiga gonar rubutu ka’in da na’in. Da ma can Makarantar ta taba shirya irin wannan gasa a tsakanin dalibanta a shekarar 2014, kuma abin ya kayatar. Wannan karon sai muka ga ya dace a yi gasar ta kasa, a kuma ba kowa dama ya shiga domin fadada tunani da kuma manufar zakulo zakakarun marubuta a duk inda suke a fadin duniya don ciyar da adabin Hausa gaba.

Ita kuwa gasar ta Pleasant Library and Books da ke Katsina tare da hadin gwiwar Makarantar Malam Bambadiya ce. Dokta Muttaka Rabe Darma, shugaban wannan kamfani shi ne Makarantar ta tuntuba domin ya agaza a ga yadda za a gudanar da gasar, kuma shi ne ya dauki nauyinta baki daya. Fatarmu da shi wanda ya dauki nauyin gasar ita ce a samar da littafi mai dauke da gajerun labarai da ke tattauna matsalolin rayuwar al’umma ba soyayya ba kurum da yanzu ta makure tunanin yawancin matasan marubuta a kasar Hausa. Sa’annan kuma burinmu a samar da labarai ne masu dan dama, ba littafi guda ba, ta yadda za a jawo hankalin matasa su rumgumi karatu da kyau.

Ko za ka yi mana bayani dalla-dalla na yadda gasar za ta gudana wato maudu’inta, su wa suka cancanci shiga, zuwa yaushe za a fara da rufewa?

Maudu’in gasar ya ta’allaka ne kan batutuwan da suka shafi talauci, wato abubuwan da suka shafi asalin samuwa da matsalolin talauci da yadda talauci ke bayyana a cikin gidaje da unguwanni da garuruwa da birane da kuma kasa, musamman a Najeriya. Haka kuma ana bukatar ganin abubuwan da talauci ke haddasawa da yadda za a iya rage radadin talauci ko magance talauci. Daga cikin ka’idojin shiga gasar; ana bukatar masu sha’awa da su aiko da tsakuren labari mai dauke da kalmomi 500 zuwa ranar 15 ga watan Oktoba, 2017. Za a tace da zabar 45 daga cikin tsakuren labaran da aka aiko wadanda suka fi burgewa a watan Disamba, 2017. Daga nan za a nemi masu wadannan labarai guda 45 da su turo cikakkun gajerun labaran nasu, wadanda za a mika ga alkalan gasar don zabar zakakuran gasar su 3 da kuma wadansu 12 da suka burge a watan Janairu 2018. Za a bayyana wadanda suka lashe gasar a watan Fabrairu, 2018 da yardar Allah. Domin karfafa ’yan gasar, za a ba da tukwicin N55,000 ga na daya, N35,000 ga na biyu sai N25,000 ga na uku. Sauran wadanda suka yi na 4 zuwa 15 za a ba kowannen su tukwicin N12,500, za a kuma tace da tsara da kuma buga labaran da suka ci gasar, tare da sauran 12 da suka burge, a kuma kaddamar da su a wani dan kwarya-kwaryar biki da za a shirya a Katsina da yardar Allah.

Bayan kammala wannan gasar, me kuma zai biyo bayanta?

Wannan gasa kamar somin-tabi ce, wasu irin ta za su biyo baya. A halin da ake ciki ma mun saki gasa ta biyu, wadda wannan kamfani na Pleasant Library and Books Katsina ya sake daukar nauyin ta, sai dai ita an hada da kwas ne da bita ga wadanda za su cinye gasar su 20. Makasudin wannan gasa ita kuma domin a tattara marubuta a wuri daya ne a koya musu dabarun tsara da shirya labari da kuma sanya salo da adanta labarai, daga baya a sake su, su koma gida domin gina labaran nasu da za su shafi ilimin kimiyya da lissafi da Ingilishi. Wannan wata sabuwar kafa ce ta samar da labarai da za su taimaka wa yara ’yan Firamare da kananan Sakandare wajen kara fahimtar wadannan darussa.

Haka kuma Makarantar Malam Bambadiya ta dukufa wajen ganin ta samu hadin kan wasu daga cikin mutane ko kamfanoni don a hada karfi da karfe waje daya don ciyar da wannan harka gaba. Makarantar tana nan tana kokarin fito da littattafan da ta rubuta da kuma tsarawa kamar littafin ’Yan Yau, wanda yake littafi ne mai dauke da labarai don yara kanana (har da manya masu sha’awa) dangane da matsalar na’urorin zamani. Da kuma littafin Jamhuriyar Mabarata, mai dauke da labarai kan matsalolin bara a kasar Hausa. Akwai kuma littafin Alfiyyar 2015, wanda shi kuma na rubutacciyar waka ne da daliban Makarantar suka tsara domin taskace siyasar Najeriya daga 1999 zuwa zaben 2015. Ga kuma ci gaba da fitar littafin DARE DUBU DA dAYA da muka sake wa fassara da tsarawa. A halin yanzu Mujalladi na daya ya fita, mun kuma kammala aikin na biyu, ana kan uku. Fatarmu ita ce mu fitar da duk mujalladai 12, dauke da labaran dare dubu da daya baki daya.  

Ko akwai sauran bayanai da suka danganci gasar nan, da ban tambaye ka ba?

Eh to ba a rasa ba. Ita wannan gasa ba daga kamfanin Pleasant Library and Books kadai za a dinga jin duriyarta ba, ba kuma kan rubutun labarai kadai za a mayar da hankali ba, muna da niyyar shirya wasu kan rubutattun wakoki da wasan kwaikwayo da wakokin baka da na fina-finai da tattara tatsuniyoyi da sauran su. A halin yanzu muna tattaunawa da shirin tuntubar mutane irin su Farfesa Abdalla Uba Adamu na Jami’ar NOUN da Farfesa Mahmoud Yakubu, Shugaban INEC da Malam Mannir dan’ali na Trust/Aminiya da Dokta Mahadi Shehu na kamfanin Dialogue da matar Sarkin Kano, Sanusi domin ganin an samu wadansu kafafen na agaza da ciyar da adabin Hausa gaba.

 

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta