Burina a daina samun mutuwar jarirai lokacin haihuwa – Mairo Rabi’u Sharif
Hajiya Mairo Rabi’u Sharif, sananniya ce kuma gogaggiyar jami’ar kiyon lafiya a Jihar Sakkwato wadda ba ta da wani kudiri da ta sanya a gaba kamar taimakon mata da yara kan harkokin rayuwa da kiwon lafiyarsu. A kullum za ka same ta cikin hidimar mutane. Kan haka Aminiya ta tattauna da ita kan abin da […]
Hajiya Mairo Rabi’u Sharif, sananniya ce kuma gogaggiyar jami’ar kiyon lafiya a Jihar Sakkwato wadda ba ta da wani kudiri da ta sanya a gaba kamar taimakon mata da yara kan harkokin rayuwa da kiwon lafiyarsu. A kullum za ka same ta cikin hidimar mutane. Kan haka Aminiya ta tattauna da ita kan abin da ya shafi rayuwarta gaba daya.
Tarihina
Sunana Mairo Rabi’u Sharif an haife ni a Jihar Sakkwato a 1968, na yi karatun Firamare a makarantar firamare ta Muhammad Bankanu daga 1971 zuwa 1977, na yi Kwalejin Malanta ta Mata da ke Bodinga (WTC) a 1977 zuwa 1982, daga nan na wuce makarantar ungozoma a Kaduna a 1987 zuwa 1990, da na kammala sai na sake dawowa Sakkwato inda na yi aure, a nan ne na shiga Makarantar Kiwon Lafiya ta Sakkwato (School of Nursing) a 1993 zuwa 1996. Na sake komawa Kaduna a Makarantar Kimiyya da Kere-Kere na yi kwas kan jarrabawar ma’aikatan gwamnati (Cibil Serbice Edamination).Sannan ina da digiri da na yi a Jami’ar Karatu Daga Gida (Open Unibersity), kuma na je Jami’ar Maradi ta kasar Nijar inda a halin yanzu na rubuta jarrabawar karshe ina jiran sakamako.
Na yi ayyukan gwamnati da yawa, na zauna a dakin haihuwa na Asibitin Kwararru tun 1982 har zuwa 1996, daga nan na zama jagora a dogon dakin mata (Female ward) shekara daya. Na koma Asibitin Mata na Maryam Abacha a nan Sakkwato na zama jagora a wurare daban-daban kamar haka; jagorar dakin haihuwa, jagorar bangaren masu fama da cutar yoyon fitsari (BBF) da jagorar kula da masu juna biyu (ANC).
Bayan nan na sake dawowa Asibitin Kwararru na Jiha a matsayin mai kula da bangaren Muhimman Mutane (Amenity), bayan shekara biyu aka dauke ni na koma Hukumar Kula da Lafiya Matakin Farko a bangaren Tsarin Iyali na yi shekara daya a wurin. Na halarci kwasa-kwasai da yawa a Najeriya da wajenta sama da 13, tare karbar lambobin yabo.
Kalubalen aiki
Ina wayar da kan mata kan zuwa asibiti domin kula da juna biyu har zuwa haihuwa da bayar da nono a kammale wata shidan farko ba tare da ba jariri ruwa ba muna shan wuyar samun hadin kan mata domin wadansu na ganin akwai wahala. Haka kuma muna wayar da kansu kan yadda ake son a yi wa cibin yaro, muna shiga karkara tare da ba su tallafi ko bashi. Saboda gaskiya wadansu maza da yawa ba su taimakon matansu ga zuwa asibiti, muna musu bayanin muhimmancin zuwa asibiti, wadansu ba su canja halinsu wayar da kan mutane da fadakar da su ga abin da zai taimaki rayuwarsu jan aiki ne kafin su fahimta su gane ba kai ne za su taimaka ba in suka yi su ne masu riba.
Misali akwai wani gari da ake kira Kaurar Wanke a Karamar Hukumar Shagari na samu labarin akwai wata yarinya da aka yi wa aure aka zo za a cire mata gurya aka samu matsala aka kwashe mata al’aura gaba daya sai wurin ya koma da kashi da fitsari duk a wuri daya yake fita. Mijinta ya rabu da ita kan matsalar ta koma gida gaban iyayenta haka take ta fama, da na je garin domin in dauko yarinyar a yi mata aiki mahaifanta sai da suka ce in ba su mako daya su yi shawara haka na dawo. Bayan na koma da kyar suka ba da yarinyar na zo Asibitin Maryam Abacha da ita aka yi mata aiki ni ke kula da ita har ta ji dama na dauki yarinyar nan na mayar musu tare da abin da ya sauwaka ta ci gaba da kula da kanta, bayan dan lokaci da na mayar da ita na bincika sai aka gaya min ai ta koma wajen mijinta har ta yi haihuwa uku.
Burina a rayuwa
Har yanzu burina bai cika ba, ina son in ga an daina samun mutuwar jarirai a wurin haihuwa duk da cewa a yanzu lamarin ya ragu. Sannan matasanmu da ke shaye-shaye su daina, matan da ba su yi karatu ba a rika wayar da kansu kan fannonin rayuwa. Wannan buri ne ya sanya a kullum ba ni hutawa a jikina da zuciyata, kullum ina cikin aikin yadda zan ga na cika burina da ikon Allah ko ba na a raye ina fata al’ummata su samu abin da nake so.
Abin da nake son a tuna ni da shi
Ina son a tuna ni da cewa lokacin nake raye ni mace ce mai son taimaka wa mata ta fannin ilimi da lafiya musamman yadda Sakkwato za ta iya gogayya da wasu jihohi takwarorinta. Sai ka ga in mun je wasu jihoji yin aiki ana cewa mu ba daga Sakkwato muke ba yadda aka ga muna gabatar da bayananmu na ilimi domin ganin jiharmu ba ta koma baya ba. Ina son in taimaka wa mata ’yan uwana su tashi tsaye su san ’yancin kansu, su taimaki ’yan uwansu mata. Duk wadda take da abin da za ta iya taimaka wa wata ta yi, ina jin dadin yadda ‘yar autata ta biyo ni a harkokin jinkai da son taimakon al’umma, na kara samun natsuwa cewa ko bayan raina ayyukan da nake yi na taimakon al’umma ba za a bari ba, don bayana za su dora
daga inda zan tsaya. Hakan ma zai sa mutane su ci gaba da tunawa da ni da yi min addu’ar samun rahamar Allah.
Wadda nake koyi da ita.
Uwargidan Gwamnan Jihar Sakkwato Hajiya Mariya Aminu Waziri Tambuwal ce nake koyi da ita domin mace ce da ta zo kan mulki da zimmar son ta taimaka wa mata fiye da yadda ake zato. Ina koyi da ita yadda take shiga karkara tana taimaka wa masu fama da cutar yoyon fitsari da gajiyayyu da talakawa. Halayyarta ta son mutane da karimci da girmama mutane ina koyi da su kuma ta zamar min abar koyi koyaushe lallai ita uwar marayu ce.
Tarbiyyar mata matasa a yanzu
Tarbiyyar mata matasa ban gamsu da yadda take a yanzu ba, domin gaskiya samari a yanzu sai addu’a ba mai taimakonsu a bangaren rayuwa da tarbiyya komai an bar shi sai gwamnati, ga masu kudi muna da su amma ba su taimakawa. Dole ya kamata a tashi tsaye kan matasan nan, mai karatu ya yi wanda zai yi sana’a shi ma a taimaka masa, a raba su da harkar shaye-shaye, maza da matan.
Shawararta ga mata
Mata musamman masu juna biyu su rika zuwa awon ciki da kula da tarbiyyar ’ya’yansu, ya kamata mahaifiya ta sani ita uwa ce kada ta bari wannan kambin ya fadi kasa ko ya fita daga hannunta. Ta rike kwarai kada ta bari duniya ta karbe mata ’ya’ya, ta jajirce lallai sai ’ya’yanta sun zama masu amfani ga kansu da duniyarsu.
Kasashen da nake son ziyarta
Ina son zuwa Amurka domin in ga yadda suke rayuwa da harkokin sha’anin lafiyarsu ina son in karo ilimi ta hanyar ganin yadda suke lamurransu. A Afirka kuma ina son zuwa Masar in ga yadda suke kula da masu juna biyu domin in karo ilimi in kawo nan gida domin kara ci gabanmu gaba daya.