Burina fito da fasahar matasanmu – Hajiya Halima Idris

Hajiya Halima Idris, Ita ce Babbar Mai Taimaka wa Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-rufa’i kan Cigaban Fasaha da kirkire-kirkire (Creatibe Art and Debelopment). A cikin wannan tattaunawar da ta yi da Aminiya, Halima ta bayyana yadda ofishin nata ke zakulo matasa masu fasaha a bangarori daban-daban don tallafa masu a gwamnatance. Sannan ta ce […]

Burina fito da fasahar matasanmu – Hajiya Halima Idris

Hajiya Halima Idris, Ita ce Babbar Mai Taimaka wa Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-rufa’i kan Cigaban Fasaha da kirkire-kirkire (Creatibe Art and Debelopment). A cikin wannan tattaunawar da ta yi da Aminiya, Halima ta bayyana yadda ofishin nata ke zakulo matasa masu fasaha a bangarori daban-daban don tallafa masu a gwamnatance. Sannan ta ce burinta shi ne duniya ta san da fasahar matasan Jihar Kaduna da ma Arewa. A sha karatu lafiya:

Aminiya: Hajiya mu fara da jin takaitaccen tarihinki.

Halima: Sunana Hajiya Halima Idris. Na yi firamare a Kaduna Capital School. Sannan na yi Kwalejin  Gwamnatin Tarayya da ke Bakori a Jihar Katsina. Sannan na yi digiri  a Jami’ar Abuja. Sannan na zarce bautar kasa (NYSC) a Jihar Ogun. Bayan haka na samu aiki a Babban Bankin Najeriya (CBN) a Abuja. 

Na yi abubuwa da dama da suka shafi taimakon jama’a cikin kungiyoyi kamar Muslimah Global Foundation. Kuma na yi wa kungiyar fasaha ta Arewa wato Arewa Creatibe Industry (ACI) da dai sauran kananan kungiyoyi, haka wanda ba sai na kawo sunana ba, amma za ka same ni ko uwar kungiyar ko kuma mamba, duk don taimakon jama’a, musamman wadanda ba su da galihu. Sannan kuma a kKdancin kasar nan akwai kungiyoyi da jama’a wadanda ke cikin farfajiyar kirkire-kirkire da fasaha wato Creatibe Industry.

To cikin ikon Allah Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmed El-rufai ya ga aikina cikin tarurrukan da na yi, sai ya ba ni aikin taimaka masa ta hanyar fito da koma taimaka wa wadanda suke da basirar, amma babu wani gwamnati da ta taba kallonsu a kan abun da Allah Ya yi masu baiwarsa. Ni ce ta farko da aka taba baiwa wannan mukami kuma a matsayina na mace kuma uwa, na san abun da ya kamata na yi in da na ne Allah Ya yi wa wannan baiwar, wato sai inda karfina ya kare wurin taimaka masa.

Aminiya: Hajiya kin yi fice a wannan aiki na fito da taurari wadanda Allah Ya yi musu fasaha amma ba a san su ba. Shin me ya bambanta wannan ofis da gwamnan Kaduna ya b aki da kuma irin ayyukan da kungiyar ki ta yi a baya?

Halima: Babu bambanci sai dai maimakon aiki da kungiya, wannan aiki na gwamnati ne. Kuma duk lokacin da aka yi maka rajista, to ka shiga cikin tsarin (record) na gwamnati kenan. Misali mun yi wa mutanen da ke cikin Jihar Kaduna rajista daga kananan hukumomi 23, sannan muka bude kafar yin rajista ta yanar gizo da kuma kalilan da suka biyo ta ofis. Mun samu mutum fiye da dubu 38 a halin yanzu. Bayan nan yanzu mun gane kowace karamar hukuma mene ne bukatarsu ta wannan ofis, sannan sai muka duba cewa su wane ne ke dinki, rubuce-rubuce, kera tukunya da dai sauransu.

An gama wannan yanzu sai koyar da kwarewa a kan sana’ar, su kansu wadanda suke wannan tsarin yadda za su yi fice da kuma kara wa sana’ar tasu armashi da kima, daraja da kuma yadda za a rika tallafawa, watau (Branding, Packaging da Promotion). Akwai tsarurruka da gwamnatin Malam Nasiru ta yi sosai, amma da ma babbar matsalar rashin sanin wadanda suke bukatar ne.

Muna nema masu hanyoyi na tallafa masu, ko da rashin lafiya ko mutuwa ta samu. Muna neman bankuna da suke bada tallafi a kan masu wannan fasaha. Sannan kuma sauran hanyoyi da gwamnati za ta samu a tsarinta na ayyuka, to amma ka ga kungiya ba ta da wannan karfin sai dai gwamnati, kuma Mai Girma Gwamna ya fahimci amfanin wadannan mutane, domin kasashe kamar su Chaina, Indiya da su Amurka ai ba ma’aikatan gwamnati ba ne suka bunkasa su, sai masu fasaha da basira. Wannan yana daga cikin dalilan yin wannan ofis don wadanda ba su da ubangida sun samu uwargida a gidan gwamnatin Malam Nasiru.

Aminiya: Kenan wannan na nuna cewa kun maida hankali ga Jihar Kaduna kadai ne ko kuwa aikin naki zai taba matasan da ke wasu jihohin musamman na Arewa?

Halima: Gaskia Kaduna ne kawai, to amma harkar bunkasa da kuma yi masu hanyoyi na san gwamna zai so a gayyaci wasu masu basira don taimaka masu a matsayinsu na ’yan Arewa. Abun da ya samu Kaduna mai kyau ko marar kyau za ka ga dole ya shafi wasu jahohin, tunda duk sunanmu Arewa. To sai dai ba zuwa za mu yi muna nema ba, amma in ta kama lallai za mu taimaka. Kamar misali a samu wani ya yi kawataccen abu, sannan mu a gwamnatance muna da hanyar taimaka wa ta wani ofis a gwamnatin tarayya ko kamfani na wata kasa. Za a iya neman yardar gwamnansu da sauran ma’aikatansa, idan sun amince domin su ne dole za su ba da goyon bayansu.

Aminiya: Wacce hanya ofishinki yake bi wajen zakulo wadannan matasa daga kananan hukumomin Jihar Kaduna?

Halima: Mun bi ta hanyar kananan hukumomi ne da ofisoshin kantomomi, sannan kuma akwai kungiyoyi masu zaman kansu da dama.

Aminiya: Idan muka koma baya, mene ne za a iya cewa ya ja hankalinki har kika ga dacewar karfafa wa matasanmu gwiwa tun gabanin shigowarki wannan ofis?

Halima: Tun kafin ofis din nan kamar yadda na ce na yi kungiyata, amma babban dalilina shi ne matsaloinmu da ke damun mutanenmu masu fasaha. Kuma ina lura da abubuwan da wasu kasashe suke yi da kuma irin namu baiwar. To sai na fara binciken dalilin da muna da abubuwan alfahari musamman a Arewa, amma kamar babu komai. Masu basirar sun koma sun bi hanyar lalacewa, don babu karfin gwiwa da tallafi. Na gano duk matsalolin da kuma mafita har yadda gwamnati za ta rika amfana da su, ba sai sun roki kowa ba. Wannan yana cikin dalilina, amma kuma ina son yau in ga duniya ta san da zaman mutanenmu a harkar fasaha da basira. Duk inda muka shiga a rika alfahari da dan Najeriya ba zaginmu ba. Sannan kuma ina son duniya ta san al’adun ‘yan Arewa na hankali, azanci da son zaman lafiyarmu.

Aminiya: Ta ina gwamnati za ta amfana da wadannan matasan kamar yadda kika bayyana?

Halima: Ai duk inda mutane suka dogara da kansu, suka samu sana’a, suka tallata kansu a duniya da sana’arsu, to gwamnati ta ci riba babba. Sannan duniya za ta zo neman kayan da aka yi a Nijeriya, ka ga wannan ma babbar riba ce, domin dole da kudinsu za su zo Najeriya. Duniya za ta fara kallon kasar da idon kima da daraja, saboda ayyukan wasu jama’a masu fasaha.

Aminiya: Kamar wadanne ayyukan fasaha ne suka fi jan hankalinki daga matasan namu da kike fatan duniya ta sani?

Halima: Fashion, wato kayanmu na Arewa ko na gargajiya ko na zamani, in dai a Arewa ne. Sai masu kirkire-kirkire na hannu kamar su faifai, ludayi, tukunya, fasahar waka da masu dirama. Amma wanda suke nuna darajarmu, ko kan fitattun mutanenmu ne da suka gabata. Haka nan masu fenti da sauran kayan gyaran gida, takalma da jakunkuna da sauransu.

Aminiya: Kasancewar ki mace, wannan na nuna cewa kin fi baiwa mata muhimmanci kenan ko kuwa?

Halima: A’a. Ai wannan aiki na maza da mata da yara da kuma masu lalura ne. Saboda haka ba aikin mata na ke yi ba domin suna da ma’aikata musamman. Ita basira ba ta ga shekaru ko jinsi. Duk wanda ya fada tsarin nan, to yana ciki.

Aminiya: Ko wane tallafi Gwamnatin Kaduna ke baiwa matasan kawo yanzu?

Halima: Ai matasa suna da ma’aikata kamar yadda kowa ya sani. Amma abun da gwamnatin Malam Nasir El-Rufai ta yi yanzu shi ne, gano ciwon mutanen da suka fada karkashin wannan ofis na bunkasa kirkire-kirkire da fasahu, sannan yanzu ana kokarin kawo maganin ciwon ne. Misali shi ne samun inshora da ya shafi lafiya ko mutuwa. Sannan samun kamfanoni ko masana’antu da wasu jakadun gwamnatoci masu tallafa wa masu irin wannan sana’a da kuma wasu hanyoyi da suka shafi bashin kudi da sauransu. Kwanan nan in Allah Ya so zamu yi kasuwar duniya na mutanen wannan ofis kawai, wato wadanda aikin ofis din ya shafe su. Muna son su fito kwai da kwarkwata domin nuna wa duniya basirarsu, za mu je yankunan Kaduna guda ukun kowanne zamu yi kwanaki don baje kolin.

Aminiya: Hajiya wane bangare na fasahar matasan ya fi kayatar dake?

Halima: Gaskiya kowanne yana ba ni sha’awa, amma babban abunda na fi so shi ne yadda suka tashi da gaske domin su tsaya da kafafunsu ba tare da mutuwar zuciya ba.

Aminiya: A karshe mene ne kiranki ga matasa baki daya?

Halima: Matasa su yi amfani da basirarsu da Allah Ya ba su ta hanya mai kyau. Duk abun da mutum ya yi kansa ya yi wa, don haka bata rayuwarka ta hanyar da ba ta dace ba a kan mutum za ta koma. Kowa ya duba iya abun da zai iya daidai gwargwado ba sai ka yi maula ko roko ba, har zuciya ta mutu. Najeriya kasarmu ce baki daya. Duk abun da ya same ta mu zamu kwana a ciki.