Burina in bude babbar makera a Najeriya -Alshaikh dankogenat

Wani mutum da ke sana’ar kira a Legas, mai suna Alshaikh dankogenat ya ce burinsa, a sana’ar, shi ne ya bude katafariyar masana’antar sarrafa karafuna.Alshaik dankogenat, dan asalin kasar Mali da ke zaune a kasuwar Alaba a Legas ya ce ya kai fiye da shekara 20 yana kira a Najeriya. “Tun ina karami na koyi […]

Burina in bude babbar makera a Najeriya -Alshaikh dankogenat

Alshaikh Dankogenat a bakin sana’rsa ta kira. A gefe kuma samfurin abubuwan da yake kerawa ne wadanda suka hada da takubba da almakusa da asake da kuma zobba. Alshaikh Dankogenat a bakin sana’rsa ta kira. A gefe kuma samfurin abubuwan da yake kerawa ne wadanda suka hada da takubba da almakusa da asake da kuma zobba. Wani mutum da ke sana’ar kira a Legas, mai suna Alshaikh dankogenat ya ce burinsa, a sana’ar, shi ne ya bude katafariyar masana’antar sarrafa karafuna.
Alshaik dankogenat, dan asalin kasar Mali da ke zaune a kasuwar Alaba a Legas ya ce ya kai fiye da shekara 20 yana kira a Najeriya. “Tun ina karami na koyi sana’ar kira kuma na fi shekara 20 ina kira a nan kasuwar Alaba. Shi ya sa ni burina a nan gaba shi ne na kafa wata babbar masa’anta da zan rika sarrafa karafuna ta hanyar da nake so, kuma na rika kera abubuwa iri-iri da mutane za su amfana da su ta yadda tattalin arzikin kasar nan zai bunkasa, kuma mutane su sami ayyukan yi”.
dankogenat ya ci gaba da cewa samun kudin da zai rika cin abinci da biyan bukatun yau da gobe shi ne babban ci gaban da ya samu a sana’ar.
Sai dai a ganinsa, karancin kayan aiki kuma shi ne babbar matsalar da ke ci masa tuwo a kwarya. “Gaskiya ba mu da isassun kayan aiki, duk abin da ka gani, mu ne muke yi da kanmu kuma mu ne muke gyarawa. Muna bukatar injina da na’urori na zamani da za mu rika sarrafa karafuna da wasa wukake, amma saboda karancin kudi mun kasa saya”. Inji shi.
Ya bayyana cewa sukan kera takubba ta farin karfe da kanana wukake da matsakaita da zobba a kan farashi daban-daban.
Ya ba da misali da takobin farin karfe da suke sayarwa a kan Naira dubu 100 da kananan wukake a kan Naira dubu 30 da kuma zobba a kan Naira dubu uku.
Ya bayar da tabbacin cewa ba sa amfani da wani magani don rage radadin wutar da suke kira da ita, amma ya bayyana cewa sukan sha madara don tana taimaka musu danagane da rage zafin wutar da ke shiga jikinsu. “Idan mutum yana aiki da wuta, to yana da kyau idan ya kammala aiki ya sha madara saboda tana taimaka wa duk makeri da wanda yake aiki da wuta, yau da gobe”. Inji shi.
Makeri dankogenat ya bayyana cewa ya koya wa yaransa da dama sana’ar kira da har yanzu suke cin abinci da ita. Sai dai ya ja hankalin matasa kada su raina sana’ar kira don, a cewarsa, tana da amfani sosai, musamman wajen samun rufin asiri.

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna